Yanzu-yanzu: Ba rikicin APC ya damu talaka ba, yan jarida na batawa kansu lokaci kan rikicin APC, Buhari

Yanzu-yanzu: Ba rikicin APC ya damu talaka ba, yan jarida na batawa kansu lokaci kan rikicin APC, Buhari

  • Daga Landan, Shugaba Buhari ya bayyana bacin ransa kan rikicin shugabancin dake gudana a jam'iyyar APC
  • Zaku tuna cewa Gwamna El-Rufa'i yace Buhari ne ya bada umurnin tsige Mai Mala Buni matsayin shugaba
  • Hukumar INEC ta ce ita Mai Mala Buni ta sani matsayin Shugaban jam'iyyar APC har yanzu

Shugaba Muhammadu Buhari ya cacccaki kafofin yada labarai kan bata lokaci wajen bada rahotanni kan rikicin da ya barke a jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

A jawabin da Buhari da kansa ya saki ranar Asabar, ya yi kira ga yan jarida su daina batawa kansu lokaci kan rikicin APC.

Buhari
Yanzu-yanzu: Ba rikicin APC ya damu talaka ba, yan jarida na batawa kansu lokaci kan rikicin APC, Buhari Hoto: Presidency
Asali: Depositphotos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Inyamuri nike son ya zama shugaban kasa a 2023, Obasanjo

Buhari yace:

"A mako daya yanzu, yan jarida sun mayar da hankalinsu kan rikicin shugabancin APC - fiye da abubuwan da jama'ar Najeriya suka damu da shi."
"Abinda ya kamata su yi shine tambayar talaka abinda yake so maimakon wannan rahotanni."
"Yan jarida zasu iya tattaunawa kan halayen yan takara tare da tattauna cancantarsu, amma shisshigi cikin lamarin cikin gidan jam'iyya batawa mutane lokaci ne."
"Ba abinda ya damu yan Najeriya ba kenan. Kuma yan Najeriya sun fi damuwa da abubuwan da ke da muhimmanci."

Shugaba Buhari ya yi magana rikicin shugabancin APC da ranar babban taro

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi tsokaci kan rikicin shugabanci da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

A wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar a Facebook, shugaba Buhari ya gargaɗi jagororin APC da su guji kiran suna da cin dudduniyar junansu.

Shugaban ƙasa ya kuma jaddada cewa babban ganganmin jam'iyyar APC na ƙasa na nan daram ranar da aka tsara 26 ga watan Maris 2022.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Shugaba Buhari ya yi magana kan rikicin APC, ya gargaɗi wasu mutane

Haka nan Buhari ya roki mambobin APC da su kawar da duk wani saɓani dake tsakanin su, kuma su haɗa kai matukar suna son jam'iyyar ta cigaba da samun nasara a dukkan matakai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel