Wani Bawan Allah Mai Shekaru 36 Ya Faɗa Rijiya Ya Mutu a Kano

Wani Bawan Allah Mai Shekaru 36 Ya Faɗa Rijiya Ya Mutu a Kano

  • Wani bawan Allah mai shekaru 36 a karamar hukumar Gezawa a Jihar Kano da ya fada cikin rijiya ya riga mu gidan gaskiya
  • Saminu Yusif Abdullahi, mai magana da yawun hukumar kwana-kwana ta jihar Kano ne ya sanar da rasuwar mutumin, Nuhu Rabiu
  • Abdullahi ya ce wani Garba Ali ne ya kira ofishin kwana-kwana don neman dauki kuma suka tura jami'ansu suka ciro shi a sume amma daga bisani ya mutu

Kano - Wani mutum mai shekaru 36, mai suna Nuhu Rabiu, a ranar Talata ya rasu a Kano jim kadan bayan an ciro shi daga wata rijiya da ya fada ciki, kamar yadda The Punch ta rahoto.

Da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin, mai magana da yawun hukumar kwana-kwana a Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce a sume aka ciro mutumin daga bisani ya rasu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

Wani Bawan Allah Mai Shekaru 36 Ya Faɗa Rijiya Ya Mutu a Kano
Wani Dan Shekaru 36 Ya Faɗa Rijiya Ya Mutu a Kano. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce wani Garba Ali ne ya kira su ya sanar da faruwar abin daga nan kuma suka tura jami'ai cikin gaggawa.

"A yau Talata 8 ga watan Maris na 2022, hukumar mu, ta samu kiran neman dauki misalin karfe 1.45 na rana daga wani Garban Alin a Hadejia Road Gunduwawa, Karamar Hukumar Gezawa.
"Lokacin da mutanen mu suka isa wurin misalin karfe 2.10 na rana, sun tarar da cewa wani mutum mai shekaru kimanin 36 ya fada wani rijiya da ke bude," a cewar Yusif Abdullahi.

Abdullahi, kamar yadda The Punch ta rahoto ya kara da cewa an mika gawar mammacin ga jami'in dan sanda mai mukamin constable, Abdullahi na ofishin yan sanda na gezawa.

Wani mutum mai shekaru 50 ya mutu cikin rijiya a Kano

Kara karanta wannan

Karar kwana: Jami'an kwana-kwana sun ciro gawar matashiyar da ta nutse a rijiya a Kano

A wani labarin, wani mutum mai shekaru 50, Abdulhamid Muhammad ya mutu a cikin rijiya a kauyen Sha’iskawa da ke karamar hukumar Danbatta na jihar Kano a ranar Talata.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saidu Mohammed ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya rabar wa manema labarai a ranar Talata a Kano.

A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talata a lokacin da marigayin ya shiga rajiyar domin ya ceto tinkiya da ta fada ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel