Wani mutum mai shekaru 50 ya mutu cikin rijiya a Kano

Wani mutum mai shekaru 50 ya mutu cikin rijiya a Kano

Wani mutum mai shekaru 50, Abdulhamid Muhammad ya mutu a cikin rijiya a kauyen Sha’iskawa da ke karamar hukumar Danbatta na jihar Kano a ranar Talata.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saidu Mohammed ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya rabar wa manema labarai a ranar Talata a Kano.

A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talata a lokacin da marigayin ya shiga rajiyar domin ya ceto tinkiya da ta fada ciki.

Wani mutum mai shekaru 50 ya mutu cikin rijiya a Kano
Wani mutum mai shekaru 50 ya mutu cikin rijiya a Kano. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: Matawalle ya gabatarwa Buhari gwala-gwalai da wasu ma'adinai da aka hako a Zamfara

Mai magana da yawun hukumar ya ce, "Wata Malama Ummi Muhammad ta kira mu a waya misalin karfe 4.37 na asuba ta lambar mu na ofishin hukumar kiyaye gobara ta Danbatta."

"A lokacin da aka sanar da mu abinda ya faru, mun tura jamian mu cikin gaggawa inda suka isa wurin misalin karfe 4.42 na asuba.

"An ciro gawar Muhammad daga rijiyar sannan aka kai shi Babban Asibitin Danbatta."

Hukumar ta kwana kwana ta shawarci mutane su dena jefa kansu cikin hadari, abinda ya fi dace wa shine su kira layukkan wayar kar ta kwana na hukumar kamar haka: 08107888878, 08098822631, 07051246833, da 07026026400.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa Gwamna Ganduje, ya amince da daukar malaman Qur’ani (Alarammomi) 60 a fadin makarantun Almajiranci 15 da ke jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar, Sanusi Kiru, a wani jawabi a ranar Talata, ya ce daukar malaman guda 60 a makarantun Almajiranci zai fara aiki ne nan take.

Ya bayyana cewa, “Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya amince da hakan biyo bayan wata wasika da hukumar makarantun Islamiyya ta jihar (KSQISMB) ta gabatar a ranar Litinin.

“Daukar wannan aiki ya sake nuna jajircewar gwamnan wajen kawar da bara a titi da kuma rashin ka’ida wajen kafa makarantun Qur’ani ba tare da samar da muhimman gine-gine da suka kamata ba.

“Wadannan gine-gine sun hada da bandaki, dakunan barci da kuma manhajar da zai sa yaran Almajirai haddace Qur’ani da sauran darusa da ake bukata cikin mutunci da tsaro,” in ji shi.

Mista Kiru ya bayyana cewa za a tura malaman guda 60 zuwa sabbin makaratun kwana na Almajiranci da aka samar a kananan hukumomin Bunkure, Madobi da Bagwai.

A cewarsa, sabbin makarantun kari ne ga guda 12 da ake da su a fadin jihar, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel