Yadda Abba Kyari ya sa nayi kashi a wando sau biyu saboda azaba, Dan jarida Agba Jalingo

Yadda Abba Kyari ya sa nayi kashi a wando sau biyu saboda azaba, Dan jarida Agba Jalingo

  • Agba Jalingo ya bada labarin irin azabar da ya sha hannun Abba Kyari da abokan aikinsa a Legas
  • Jalingo dai dan jarida ne kuma dan fafutuka da gwamnan jihar CrossRiver ya sa aka kama a shekarar 2019
  • Bayan kwanaki 180 a kurkuku, kotu ta bada belin Agba Jalingo

Mai kamfanin jaridan CrossRiverwatch, Agba Jalingo, a ranar Litinin ya bayyana irin azabtarwan da dakataccen dan sanda, Abba Kyari, yayi masa tare da yaransa.

Agba yace Kyari ya jefashi bayan mota daga Legas zuwa Calabar.

Zaku tuna cewa gwamnatin jihar Cross River ta shigar da Agba Jalingo kotu a shekarar 2019 kuma aka garkameshi a kurkukun Afokang na tsawon kwanaki 179.

Dan jarida Agba Jalingo
Yadda Abba Kyari ya sa nayi kashi a wando sau biyu saboda azaba, Dan jarida Agba Jalingo Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Katsina: Yan bindiga sun bude wuta a kan wata mota, sun kashe fasinjoji 5

A hirarsa da Vanguard, Agba ya bada labarin yadda aka garkameshi a caji ofis na rundunar IRT dake Ikeja kafin aka bada umurnin kaishi Calabar.

Yace:

"DCP Kyari da ACP Ubua sun damkeni a Legas, suka jefa a bayan motar Toyota Highlander daga Legas zuwa Calabar. Ba zan taba manta wannan abu ba."
"Sun saka min ankwa a hannu da kafa a bayan motar kamar wani Shanun da ake kaiwa kudu daga Arewa."
"Sau biyu ina kashi a wando. Na rika rokonsu su bani ruwa amma suka ki. Suka rika bugu na da gindin bindiga suna cewa 'barawo, zamu kasheka yau."

Lauyoyi 20 sun lashi takobin tsayawa Abba Kyari saboda alkhairansa sun fi sharrinsa

Akalla lauyoyi ashirin (20) sun bayyana niyyar tsayawa dakataccen dan sanda DCP Abba Kyari bisa karar da hukumar yaki da muggan kwayoyi NDLEA ta shigar kansa.

Wani lauya mai suna, Musa Shafiu, wanda yayi magana a madadin lauyoyin ya bayyanawa manema labarai ranar Laraba, rahoton NAN.

Kara karanta wannan

Yankin Yarbawa zai balle daga Najeriya ba tare da bindiga ba, Sunday Igboho

A cewarsa, cikinsu akwai manyan lauyoyi SAN guda hudu.

Lauyan yace sun yanke shawaran haka ne bisa jarumta, kokari da sadaukarwar da ya yiwa kasar nan a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel