Lauyoyi 20 sun lashi takobin tsayawa Abba Kyari saboda alkhairansa sun fi sharrinsa

Lauyoyi 20 sun lashi takobin tsayawa Abba Kyari saboda alkhairansa sun fi sharrinsa

  • Wasu lauyoyi a birnin tarayya Abuja sun ce zasu kare Abba Kyari a kotu kan laifukan da ake tuhumarsa da su
  • Tuni dai Abba Kyari ya dau hayan babban lauya kuma tsohon Antoni Janar, Kanu Agabi
  • Kyari na gurfana gaban babban kotun tarayya dake Abuja kan karar NDLEA yayinda kuma ake shirin mika sa ga Amurka

Akalla lauyoyi ashirin (20) sun bayyana niyyar tsayawa dakataccen dan sanda DCP Abba Kyari bisa karar da hukumar yaki da muggan kwayoyi NDLEA ta shigar kansa.

Wani lauya mai suna, Musa Shafiu, wanda yayi magana a madadin lauyoyin ya bayyanawa manema labarai ranar Laraba, rahoton NAN.

A cewarsa, cikinsu akwai manyan lauyoyi SAN guda hudu.

Abba Kyari
Lauyoyi 20 sun lashi takobin tsayawa Abba Kyari saboda alkhairansa sun fi sharrinsa Hoto: Abba Kyari/Facebook
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Hush-Kyari: Ministan shari'a ya yi amai ya lashe, ya wanke Abba Kyari daga zargin damfara

Lauyan yace sun yanke shawaran haka ne bisa jarumta, kokari da sadaukarwar da ya yiwa kasar nan a baya.

Shafiu yace:

"DCP Abba Kyari a karar da aka shigar gaban Alkali Inyang Ekwo na babban kotun tarayya dake zamanta a Abuja, ya karyata zargin da NDLEA ke masa na kasancewa mamban kungiyar yan kwaya."
"Kyari shirye yake ya kare kansa kan wannan sharri da aka shirya masa."

Ya kara da cewa Kyari ya yiwa kasar nan bauta matsayin dan sanda bayan kama manyan yan ta'adda a kasar nan kuma alkhairansa sun fi sharrinsa yawa.

Yadda Abba Kyari ya sa nayi kashi a wando sau biyu saboda azaba, Dan jarida Agba Jalingo

Mai kamfanin jaridan CrossRiverwatch, Agba Jalingo, a ranar Litinin ya bayyana irin azabtarwan da dakataccen dan sanda, Abba Kyari, yayi masa tare da yaransa.

Agba yace Kyari ya jefashi bayan mota daga Legas zuwa Calabar.

Kara karanta wannan

Yadda Abba Kyari ya sa nayi kashi a wando sau biyu saboda azaba, Dan jarida Agba Jalingo

Zaku tuna cewa gwamnatin jihar Cross River ta shigar da Agba Jalingo kotu a shekarar 2019 kuma aka garkameshi a kurkukun Afokang na tsawon kwanaki 179.

A hirarsa da Vanguard, Agba ya bada labarin yadda aka garkameshi a caji ofis na rundunar IRT dake Ikeja kafin aka bada umurnin kaishi Calabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel