Sun talauta ni da dana: Yadda dangin mata suka kwashe komai bayan mutuwarta, suka bar mijinta hannu rabbana

Sun talauta ni da dana: Yadda dangin mata suka kwashe komai bayan mutuwarta, suka bar mijinta hannu rabbana

  • Wani mutumin kasar Kenya ya magantu game da yadda komai ya kwace masa bayan mutuwar matarsa sakamakon cutar HIV
  • Mutumin mai suna Kassim Hemed ya bayyana cewa surukansa sun je gidansa sun kwashe komai da suke da shi bayan mutuwar matar tasa
  • A yanzu mutumin na rayuwa ne cikin talauci, kuma ya ce yana ganin kamar gazawa yayansa saboda baya iya daukar dawainiyarsu

Kassim Hemed ya shiga kuncin rayuwa bayan surukansa sun kwashe komai da suka mallaka tare da matarsa bayan mutuwarta sanadiyar cutar HIV.

Hemed ya bayyana cewa a yanzu daga shi har yaransa maza su uku suna rayuwa ne hannu baka, hannu kwarya tun 2019 lokacin da matar ta mutu.

Surukaina sun kwashe komai bayan mutuwar matata, yanzu a kasa yarana suke kwanciya, cewar magidangi a bidiyo
Surukaina sun kwashe komai bayan mutuwar matata, yanzu a kasa yarana suke kwanciya, cewar magidangi a bidiyo Hoto: Yvonne Kawira.
Asali: Original

Da shi da yaransa suna aikin karfi domin samun cin abinci koda sau daya ne a rana.

A yanzu mutumin na fama da cutar damuwa kuma yana gani kamar bai kyautawa yaransa ba saboda ya gaza daukar dawainiyar su.

Kara karanta wannan

Maula da ake tasa mu da ita yasa muke tserewa Abuja, mu sauya lambar waya, 'Yan majalisar Najeriya

Bacci a kasa

“A kasa muke kwanciya kuma wasu lokutan muna iya daukar tsawon kwanaki babu abinci. A duk lokacin da na dawo gida hannu goma sai na ji babu dadi bana ma iya fuskantarsu. Musamman na fi tausayin karamin ciki. Wasu daga cikin abokaina kan siya mani barasa ne kawai a duk lokacin da na je roko. Sai su fada mani cewa yana taimakawa wajen dauke mun tunanina,” in ji Hemed.

Mutumin wanda yaransa ke gwagwarmayar zuwa makaranta ya ce yana so ya koma kauye sannan ya fara sabon rayuwa.

“Akalla akwai fili a kauyen inda marigayiya mahaifiyata ta yi rayuwa. Zan zauna a nan yayin da nake farfadowa," ya fada ma Yvonne Kawira na TUKO.co.ke a wata hira.

Aure ya yi albarka: Hotunan magidancin da ya auri mata 2 a rana guda yayin da suke murnar cika shekara 1

Kara karanta wannan

Aure ya yi albarka: Hotunan magidancin da ya auri mata 2 a rana guda yayin da suke murnar cika shekara 1

A gefe guda, masu iya magana kan ce sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a kaiba. Tafiya dai ta fara mika tsakanin wani magidanci da ya auri mata biyu a rana daya.

A bara ne dai labarin mutumin mai suna Babangida Adamu Sadiq, ya karade shafukan soshiyal midiya sakamakon auren mata biyu, Maimuna Mahmud da Maryam Muhammad Na'ibi da ya yi a rana daya.

A ranar 6 ga watan Maris din 2021 ne dai aka daura auren masoyan. Don a haka ya shirya bikin murnar zagayowar wannan rana a jiya Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel