Kungiyar Yarbawa ta sa baki, Jamhuriyar Benin ta saki dan awaren Yarbawa Sunday Igboho

Kungiyar Yarbawa ta sa baki, Jamhuriyar Benin ta saki dan awaren Yarbawa Sunday Igboho

  • Rahoto daga majiyoyi ya bayyana cewa, an sako dan awaren Yarbawa Sunday Igboho bayan tsare shi na watanni
  • An tsare Sunday Igboho a jamhuriyar Benin tun a 2021, inda ake tuhumarsa da wasu laifuka da yawa
  • Yau dai an samu rahoton da ke cewa, wasu jiga-jigan Yarbawa sun shawo kan lamarin an sako Igboho daga Benin

Kwatano, Benin - Jaridar Punch ta rahoto cewa, Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta saki dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Ighoho bayan doguwar tsarewa da ya sha.

Hadin kan Yarbawa a kungiyoyin rajin kare hakkin Yarabawa ta Ilana Omo Oodua Worldwide ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Dan rajin kare hakkin Yarbawa ya sha dakyar
Yanzu-Yanzu: Jamhuriyar Benin ta saki Sunday Igboho bayan tsare shi na watanni | Hoto: punchng.com
Asali: Facebook

Sanarwar wadda mai magana da yawun Ilana Omo Oodua, Mista Maxwell Adeleye, ya fitar, mai taken, ‘Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta Saki Dan rajin kare al’ummar Yarabawa, Sunday Adeyemo Ighoho ga shugaban Yarbawa, Banji Akintoye; Masanin harshen Faransanci, Adeniran'.

Kara karanta wannan

Sai irin su Buhari: Osinbajo ya bayyana wanda iya zai magance matsalar tsaro a Najeriya

Har yanzu dai babu wasu cikakkun bayanai game da sakin Sunday Igboho da ke tsare a Jamhuriyar Benin tun shekarar 2021.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan sakin Igboho, Akintoye ya bayyana sakin a matsayin nasaran gaskiya akan duhu a kasar Yarbawa, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Igboho ya tsere ne daga gidansa da ke Ibadan a ranar 1 ga Yuli, 2021 lokacin da jami’an tsaro na farin kaya, DSS suka kai farmaki gidansa domin kwamushe shi.

Bayan haka, ya tsere daga kasar, inda aka kama shi a Jamhuriyar Benin a lokacin da yake kan hanyarsa ta shillawa Jamus tare da matarsa Ropo, wanda daga baya aka sake ta.

An kama Igboho ne a ranar 20 ga Yuli, 2021 kuma an tsare shi a Cotonou, Jamhuriyar Benin tun lokacin.

Lauyansa ya tabbatar da sakinsa

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Sojoji sun yi kazamin artabu da yan ta'adda, sun aika 17 ga Allah a Borno

The Cable a bayyana cewa, lauyan Igboho, Yomi Alliyu, ya tabbatar da sakin shugaban 'yan awaren na Yarbawa, inda yace:

"Ina sanar da ku cewa Cif Sunday Adeyemo, aka.Igboho Oosa, an sake shi daga gidan yari ga likitocinsa bisa yarjejeniyar cewa kada ya bar cibiyar kiwon lafiya ko Cotonou ko meye dalili.

Hakazalika, ya bayyana yabawarsa ga wasu fitattun Yarbawan Najeriya, Farfesa Wole Soyinka da Farfesa Akintoye bisa namijin aikin tabbatar da sakin Igboho.

Ba dani ba: Lauyan Sunday Igboho ya zare hannunsa a rikicinsu da gwamnatin Buhari

A wani labarin, Lauya Pelumi Olajengbesi, daya daga cikin lauyoyin da ke kare Sunday Adeyemo, shugaban 'yan awaren Yarbawa wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya yi murabus daga tawagar kare dan awaren.

Idan baku manta ba, a baya mun kawo muku rahotannin yadda gwamnatin jamhuriyar Benin ta kame Sunday Igboho ta tasa keyarsa magarkama a kasar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Neja ya dira hedkwatar APC don maye gurbin Mai Mala Buni

Daga nan ne batutuwa suka fara girma, gwamnatin Najeriya ta fara bibiyar yadda za ta dawo dashi Najeriya don gurfanar dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel