Da duminsa: Daga karshe, Buhari ya shilla Landan ganin Likita

Da duminsa: Daga karshe, Buhari ya shilla Landan ganin Likita

  • Bayan dawowa Najeriya daga Kenya maimakon Landan, Shugaba Buhari zai tafi ganin Likitocinsa
  • Kowace shekara sai shugaban kasan ya tafi kasar Birtaniyya duba lafiyarsa duk da makudan kudaden da gwamnati ke ikirarin zubawa asibitin fadar shugaban kasa
  • Tun bayan ciwon kunnen da yace yana fama da shi, har yanzu yan Najeriya basu san abinda Buhari ke zuwa Landan ba
  • A shekarar 2021, Shugaban kasan ya bada kwangilan ginin asibiti na musamman cikin fadar Aso Villa

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari daga karshe ya tashi daga birnin tarayya Abuja inda ya nufi birnin Landan, kasar Birtaniya a yau Lahadi.

Zaku tuna cewa a makon da ya gabata an shirya Shugaban kasan zai tafi Landan daga kasar Kenya bayan halartan taron majalisar dinkin duniya a Nairobi.

Da duminsa: Daga karshe, Buhari ya shilla Landan ganin Likita
Da duminsa: Daga karshe, Buhari ya shilla Landan ganin Likita
Asali: Twitter

Adesina yace Shugaba Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Karamar ministar yanay, Sharon Ikeazor; NSA Manjo Janar Babagana Monguno; DG na NIA, Ambasada Rufai Abubakar, da Shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.

Kara karanta wannan

Inyamuri nike son ya zama shugaban kasa a 2023, Obasanjo

Ya kara da cewa Buhari zai gabatar da jawabi a taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel