Yin aure kuskure ne da na tafka a rayuwata kuma ba zan kara ba, Magidanci na neman sakin matarsa

Yin aure kuskure ne da na tafka a rayuwata kuma ba zan kara ba, Magidanci na neman sakin matarsa

  • Wani mutum, wanda aure ya ganawa azaba, mai suna Miles Montego ya sanar a shafinsa na Twitter cewa zai rabu da matarsa sati mai zuwa bayan auren nasu ya ki dadi
  • Wallafar Miles ya janyo cece-kuce a yanar gizo, sai dai abun mamaki maza da dama sun bayyana yadda suka rabu da matansu ciki kwanakin nan, bayan wadanda suke kokarin yin hakan
  • Yayin martani ga wallafar Miles, wata mata ta ce: "Nima har yanzu ina tsoron aure...nawa ya faru ne a 12 ga watan Agusta 2015"

Wani mutum dan Afirika ta kudu, Miles Montego, ya azabtu bayan aurensa ya ki dadi. Mutumin da ya taba auren ya jawo cecekuce a kafafan sada zumuntar zamani na Twitter, bayan ya wallafa abunda ya siffanta da babban kuskuren da ya taba aikatawa.

Kara karanta wannan

Mutane su gama aibatani a zo ranar lahira su ga na shige Aljanna na barsu - Umma Shehu

Miles Montego ya ce, auren da yayi shi ne babban kuskuren da ya taba tafkawa.

Yin aure kuskure ne da na tafka a rayuwata kuma ba zan kara ba, Magidanci na neman sakin matarsa
Yin aure kuskure ne da na tafka a rayuwata kuma ba zan kara ba, Magidanci na neman sakin matarsa. Hoto daga @Milesmontego
Asali: Twitter

Mutumin ya sanar da cewa, yanzu bai da aure. Ya wallafa hoto daga na shagalin bikin shi tare da sako mai karya zuciya, wanda ya ce:

"18 ga watan Maris ne ranar rabuwar aure na. Bisa ga babban kuskuren da ba zan taba maimaita wa ba..."

Wallafar Miles ta janyo tsokaci daban-daban a yanar gizo, wanda ya ba mutane mamaki matuka, inda maza da dama suka bayyana yadda suka rabu da matansu, bayan wadanda ke shirin yin hakan ba da jimawa ba.

@Leratolameric yayi tsokaci: "Mata ta ta fadamin cewa, tana so ta rabu dani saboda ni talaka ne. Da zafi, idan mace ta fada maka haka kai tsaye, ashe wani na bata kudi... A lokacin ban dade da warkewa daga cutar kansa ba, yanzu kuma rabuwa."

Kara karanta wannan

Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

@Mxolisi Makhanya yayi nazari: "Kayi hakuri 'dan uwana. Nima zan biyo sawun ka bada jimawa ba... Babban kuskuren da ba zan taba maimaitawa ba."
@DazaDLG yayi tsokaci da: "Duniya ce ta amsa kudin don kawai ka samu damar rabuwa da ita. Barta ta tafi zaka farfado da mai son ka na gaske."
@Hazel Mahazard ya ce: "A lokacin da za ka yi aure kaga alamar tabbata a farinciki har abada ko kuwa kaga jar danja amma ka yanke shawarar yin auren kawai da fatan dacewa?"
@Motlokoa ya rubuta: "Yi hakuri 'dan uwa, ba kai kadai bane, na tsinke nawa a ranar Laraba."
@Nomkhosi Keswa ta ce: "Nima haka, har yanzu tsoron aure nake. Na wa ya faru ne a 12 ga watan Agusta 2015."

Cutata aka yi, ashe tana da 'ya'ya uku na aureta - Magidanci ya sanar da kotu

A wani labari na daban, wani mai walda da ke zama a Ibadan mai suna Quozeem Owolabi, ya maka matarsa Tunrayo a gaban wata kotun gargajiya da ke zama a Ile-Tuntun, Ibadan, jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Ɗan Sanda Ya Bindige Abokan Aikinsa 6 Har Lahira A Hedkwatar Ƴan Sanda a Maiduguri

Ya bukaci da a tsinke igiyar aurensu mai shekara daya a kan abinda ya kwatanta da rufa-rufa. Ta ki sanar masa cewa tana da 'ya'ya har uku kafin su yi aure.

Bugu da kari, Owolabi ya yi korafin cewa bata sallah da azumin watan Ramadana, kamar yadda ta yi masa alkawari kafin su yi aure.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel