Cutata aka yi, ashe tana da 'ya'ya uku na aureta - Magidanci ya sanar da kotu

Cutata aka yi, ashe tana da 'ya'ya uku na aureta - Magidanci ya sanar da kotu

- Owolabi Quozeem mai walda ne mazaunin Ibadan wanda ya maka matarsa a gaban kotu bayan aurensu da shekara daya

- Owolabi ya zargi matarsa Tunrayo da caka masa, ta yi masa karyar dan ta daya da wani kafin su yi aure amma ashe uku gareta

- Ya zargeta da kin yi sallah da kuma azumin watan ramadana, akasin yadda ta yi masa alkawari kafin su yi aure

Wani mai walda da ke zama a Ibadan mai suna Quozeem Owolabi, ya maka matarsa Tunrayo a gaban wata kotun gargajiya da ke zama a Ile-Tuntun, Ibadan, jihar Oyo.

Ya bukaci da a tsinke igiyar aurensu mai shekara daya a kan abinda ya kwatanta da rufa-rufa. Ta ki sanar masa cewa tana da 'ya'ya har uku kafin su yi aure.

Bugu da kari, Owolabi ya yi korafin cewa bata sallah da azumin watan Ramadana, kamar yadda ta yi masa alkawari kafin su yi aure.

Mai korafin ya sanar da kotun cewa, Tunrayo ta yi masa karyar cewa da daya gareta da wani kafin su yi aure, amma sai ya gano uku gareta.

Matashin wanda har a halin yanzu basu haihu ba, ya zargeta da zagon kasa a kan duk kokarinsa na yi mata ciki.

"Ta shirya ganin bayana saboda tana da wasu 'ya'yan da wani mutumin. A cikin kwanakin nan, tana barin gida da safe amma sai dare take dawowa. Hakan yasa nake neman saki," yace.

Tunrayo wacce ta amince da bukatar sakin, ta musanta dukkan zargin da Owolabi ya fadi a kanta.

Ta ce, "Mutumin nan dukana yake yi akai-akai. Yana bani N300 a kowacce rana ni da 'ya'yana. Da kudina na kai shi asibiti lokacin da bashi da lafiya, amma ni da na kwanta ciwo bai damu ba."

Alkalin kotun, Henry Agbaje, ya dage yanke hukunci har zuwa ranar 30 ga watan Satumban 2020.

KU KARANTA: 'Yan daba sun kai wa tawagar Gwamnan APC hari, sun ragargaza ababen hawa

Cutata aka yi, ashe tana da 'ya'ya uku na aureta - Magidanci ya sanar da kotu
Cutata aka yi, ashe tana da 'ya'ya uku na aureta - Magidanci ya sanar da kotu
Source: Getty Images

KU KARANTA: Motocin kudin da ka kwamushe a gidanka ba za su iya siya maka Edo ba - Ikimi ga Tinubu

A wani labari na daban, wani dan kasuwa, Iga Bale, a ranar Laraba ya roki kotun gargajiya da ke Nyanya Abuja ta raba aurensa da matarsa Liza a kan cewa ta rantse sai ta gallaza masa ta mayar da shi tamkar mabaraci.

Bale ya roki wannan alfarman daga hannun kotu ne cikin takardar neman raba aure da ya shigar a kotun.

"Da jarin kasuwanci ne ya karya, na koma Abuja da zama. Na samu aiki da wani kamfani mai zaman kansa na kuma dako matata da yara na su dawo Abuja tare da ni.

"Da matata ta zo, na ce tayi maneji da karamin aikin da na samu har zuwa lokacin da babban aiki sai samu.

"Duk da cewa ta yarda, bayan kankanin lokaci sai ta fara boye abincin da ta ke siya da kudin da na ke bata.

"Tana barnatar da abinci domin dai a rasa abinda za a ci a gidan.

"Da na yi mata magana a kan hakan, sai ta ce niyyar ta shine ta kashe dukkan kudi na har sai na talauce kamar mabaraci.

"Ta zubar da cikin da ta dauka bayan watanni hudu, likitan da ya zubar mata ma soyayya su ke yi,' kamar yadda mijin ya yi ikirari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel