Wahalar Mai: Anyi rabon jarkokin man fetur a wani bikin hadimar gwamna a jihar Legas

Wahalar Mai: Anyi rabon jarkokin man fetur a wani bikin hadimar gwamna a jihar Legas

  • Mai bukin murnar bata sarauta ta yi rabon galolin man fetur ga wadanda suka halarci bikin
  • Erelu Okin ta bayyana cewa ta raba fetur ne saboda godiya da mutanen da suka samu halarci duk da wahalar man da ake ciki
  • Gwamnatin jihar Legas ta bayyana bacin ranta kan wannan abu kuma ta bada umurnin kamo matar

Yayinda yan Najeriya ke fama da matsanancin wahalar man fetur, an yi rabon jarkokin mai matsayin kyautar halartar biki a jihar Legas.

A hotunan da bidiyon da wani @ThisIsKennys ya saki a shafinsa na Tuwita, an kan yadda aka lika hotunan wanda ke bikin a jikin jarkuna da sunan "Erelu Okin Foundation Installation Party.”

Mawakin dake waka a taron ya jinjinawa wa matar da ke rabon wacce Hadima ce aba ga Gwamnan jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Mace tagari: Hoton diyar Abacha tana nuna kauna ga Buni yayin da yake cikin damuwa

Jihar Legas
Wahalar Mai: Anyi rabon jarkokin man fetur a wani bikin hadimar gwamna a jihar Legas Hoto: @ThisisKenny
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnatin jihar Legas a ranar Asabar ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan bidiyon.

Kwamishanan labaran jihar, Gbenga Omotosho, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.

Yace:

"Ko shakka babu wannan abu na da hadari kuma yana iya sabbasa asarar rayuka da dukiya. Gwamnatin jihar Legas na gudanar da bincike kan lamarin."
"Tsaron rayuka da dukiyoyin mutanen Legas na da muhimmanci ga gwamnatin Gwamna Baajide Sanwo-Olu."

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel