Mace tagari: Hoton diyar Abacha tana nuna kauna ga Buni yayin da yake cikin damuwa

Mace tagari: Hoton diyar Abacha tana nuna kauna ga Buni yayin da yake cikin damuwa

  • Diyar tsohon shugaban kasar Najeriya, Gumsu Abacha, ta wallafa hoton ta da na mjinta Gwamna Mai Mala Buni
  • A hoton da ta saka a shafinta na Twitter, an ganta tana murmushi ga maigidanta yayin da yaka mayar da martani
  • Wannan ya zo ne ana tsaka da rikicin cikin gida na jam'iyya mai mulki inda aka tumbuke mijinta daga shugabancin APC

Gumsu Abacha, daya daga cikin matan Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, ta bayyana wani hotonta tare da mijinta.

A hoton, an ga matar wacce ta kwatanta kanta da diyar janar din soja mai anini hudu, tana murmushi cike da farin ciki yayin da mijin nata yake mayar mata da martani.

Mace tagari: Hoton diyar Abacha tana nuna kauna ga Buni yayin da yake cikin damuwa
Mace tagari: Hoton diyar Abacha tana nuna kauna ga Buni yayin da yake cikin damuwa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Gumsu wacce ta saka hoton mijinta a matsayin hoton shafinta na Twitter, ta wallafa hotonsu tare da mijinta yayin da ake tsaka da rikicin shugabanci na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An kuma sace kananan yara yan shekara 4 a Keke Napep bayan tashi daga makaranta

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar Litinin da ta gabata, Gwamna Sani Bello na jihar Neja ya jagoranci lamarran jam'iyyar All Progressives Congress (APC), aikin da kowa ya san na Buni ne tun bayan da aka bayyana shi a matsayin shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar a shekaru biyu da suka gabata.

A halin yanzu Buni yana kasar waje wurin duba lafiyarsa, amma Gwamna Nasir El-Tufai na jihar Kaduna ya ce ba zai taba dawowa a matsayin shugaban jam'iyyar APC ba.

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya ce duk gwamnonin da ke goyon bayan Buni gwamnoni ne 'yan damfara.

Ba rikicin APC ya damu talaka ba, yan jarida na batawa kansu lokaci kan rikicin APC, Buhari

A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya cacccaki kafofin yada labarai kan bata lokaci wajen bada rahotanni kan rikicin da ya barke a jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta yi amai ta lashe, tace har yanzu Gwamna Mala Buni ne shugabanta

A jawabin da Buhari da kansa ya saki ranar Asabar, ya yi kira ga yan jarida su daina batawa kansu lokaci kan rikicin APC.

Buhari yace: "A mako daya yanzu, yan jarida sun mayar da hankalinsu kan rikicin shugabancin APC - fiye da abubuwan da jama'ar Najeriya suka damu da shi."
"Abinda ya kamata su yi shine tambayar talaka abinda yake so maimakon wannan rahotanni."
"Yan jarida zasu iya tattaunawa kan halayen yan takara tare da tattauna cancantarsu, amma shisshigi cikin lamarin cikin gidan jam'iyya batawa mutane lokaci ne."
"Ba abinda ya damu yan Najeriya ba kenan. Kuma yan Najeriya sun fi damuwa da abubuwan da ke da muhimmanci."

Asali: Legit.ng

Online view pixel