Wata Wuta ta lakume kayayyakin sama da miliyan N18m a siton NEMA a jihar Kano

Wata Wuta ta lakume kayayyakin sama da miliyan N18m a siton NEMA a jihar Kano

  • Wata gobara da ta tashi a siton aje kayayyaki na hukumar kwana-kwana SEMA a Kano, ta yi mummunar ɓarna
  • Shugaban hukumar Dakta Saleh Jiji, ya bayyana cewa kayan da gobarar ta kone sun kai darajar kudi miliyan N18.5m
  • Ya kuma shawarci al'ummar jihar Kano su kula da wutar daji, domin kiyaye lafiya da kuma yuwuwar tashin wuta

Kano - Wata wuta da ta tashi ranar Jumu'a da yamma a siton hukumar kai agajin gaggaywa SEMA ta lakume kayayyakin da suka kai darajar miliyan N18.5m.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wutar ta yi wannan aika-aika ne a Siton SEMA dake Mariri, ƙaramar hukumar Kumbitso, jihar Kano.

Sakataren hukumar SEMA, Dakta Saleh Jili, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin hira da manema labarai a Kano ranar Jumu'a.

Wutar Gobara
Wata Wuta ta lakume kayayyakin sama da miliyan N18m a siton NEMA a jihar Kano Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya ce lamarin ya auku ranar Jumu'a da karfe 1:00 na rana a Siton Mariri, wurin da ake aje kayayyakin taimakon wanda lamarin gobara ya shafa da ambaliyar ruwa.

Kara karanta wannan

Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

A cewarsa, azuzuwa uku na wata makaranta dake kusa da siton sun kone kurmus sanadin harshen wutar da ya tashi, wanda ya kai ga taba wurin.

Abubuwan da wutar ta ƙona

Abubuwan da wutar da cinye sun haɗa da tabarmu 450, matashi 450, abun yin nafkin na yara da manya katan 655.

Sauran kayayyakin sun haɗa da Katan ɗin Dettol 10, Kekunan ɗinki. da na aikin wuta, ragar sauro da sauran abubuwa, da suka kai kudi Miliyan N18.5m.

Vanguard ta rahoto Yace:

"Jami'an mu zasu tantance asarar da aka yi da kuma darajarsu domin miƙa wa shugabannin mu na gwamnati."

Bayan haka kuma, ya yi kira ga al'umma su yi taka tsantsan da wutar daji domin kiyaye kayan su da kuma lafiyar su.

A wani labarin kuma Dalibin da ake zargi da halaka budurwarsa ya koma mawaƙi a Kotu

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Matar makashin Hanifa Abubakar ta juya masa baya a Kotu, ta faɗi gaskiyar lamari

Wani dalibin jami'ar Jos da ake shari'a kan zargin ya halaka budurwarsa domin yin asiri ya koma mawaki a zaman Kotu.

Ana zargin dalibin Moses Okoh da kashe budurwarsa, Jennifer, a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel