Rashin mai da rashin wuta: Ku cigaba da juriya, ai ba mulkin Buhari aka fara rashin ba: Femi Adesina

Rashin mai da rashin wuta: Ku cigaba da juriya, ai ba mulkin Buhari aka fara rashin ba: Femi Adesina

  • Mai magana da yawun Buhari ya yi kira ga yan Najeriya su cigaba da hakuri kan wahalan rashin man da ake fama da shi
  • Adesina, a jawabinsa ya ce ai ba a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari aka fara wahalar mai ba
  • Yan Najeriya da dama sun nuna bacin ransu kan wannan jawabi da Kakakin shugaban kasan ya fadi

Abuja - Mista Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ba mulkin maigidansa kadai aka fara wahala da tsadar man fetur ba.

Tsawon wata guda yanzu, Najeriya na fuskantar rashi da tsadar man fetur inda mutane ke kwana da motocinsu a gidajen mai.

Femi Adesina
Rashin mai da rashin wuta: Ku cigaba da juriya, ai ba mulkin Buhari aka fara rashin ba: Femi Adesina Hoto: Channels TV
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

A jawabin mako-mako da Adesina ya saba, ya bayyana cewa yan Najeriya zasu jure saboda sun jure ire-iren wadannan matsaloli kafin lokacin mulkin Buhari.

Yace:

"An samu matsalar gurbataccen mai a baya a kasar nan. Mun kwana na tsawon kwanaki da makonni a gidajen mai kuma mun rayu. Wannan ma zamu rayu. Ko ta kaka."
"Ina kira gareku don tunatar muku da cewa abubuwa basu gurbacewa kasarmu ba."
"Rashin mai zai so ya tafi. Yan Najeriya kuwa masu godiya zasu ji dadi."

Ku kwantar da hankulanku, muna da litan mai 1.7bn: Shugaban NNPC ga yan Najeriya

Kamfanin man Najeriya NNPC ya yi kira ga yan Najeriya su daina tada hankulansu suna ajiyan man fetur saboda akwai isasshen mai a ajiye da za'a fitar.

Dirakta Manaja na NNPC, Mele Kyari, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a Abuja ranar Laraba bayan ganawarsa da kungiyar ma'aikatan man fetur da kungiyar direbobin tankan mai (PTD).

Kara karanta wannan

Birbishin rikici a Pleateau yayinda aka hallaka Shanu 100 ba gaira ba dalili

Sauran kungiyoyin dake hallare a ganawar sun hada da kungiyar yan kasuwar mai na Depot, DAPMAN, da kungiyar manyan yan kasuwan mai MOMAN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel