Ma’aikata 4 da aka yadda da su, sun yi amfani da ATM, sun sacewa banki Naira miliyan 800

Ma’aikata 4 da aka yadda da su, sun yi amfani da ATM, sun sacewa banki Naira miliyan 800

  • Hukumar EFCC ta na shari’a da wasu ma’aikata da ake zargin sun daukewa banki miliyoyin kudi
  • Wadanda ake tuhuma su ne: Olusegun Babasola, Abisola Ahmed, Uchechukwu Uma, sai Jude Aphaeus
  • Wani shaida da lauyan EFCC ya gabatar a gaban kotu ya tona yadda ma’aikatan suka yi gaba da N870m

Lagos - Wani jami’in bincike da ke aiki da hukumar EFCC ya fadawa kotun Legas yadda wasu ma’aikatan banki suka saci miliyoyi na banki da jama’a.

Premium Times ta ce EFCC ta na zargin wadannan ma’aikata da dauke Naira miliyan 874 da wasu suka kawo ajiya a bankin na su, an yi wannan ne a 2019.

Chimdinma Peter shi ne shaida na uku da EFCC ta gabatar a shari’ar da ake yi da wadannan ma’aikata hudu a kotun binciken laifuffuka na musamman.

Kara karanta wannan

Minista ya yi wa daliban jami’a albishir, ASUU ta kusa janye yajin-aikin da ta shiga

Mai magana da yawun bakin EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar da jawabi, yana cewa Chimdinma Peter ya yi bayanin abin da ya sani a zaman kotu da aka yi.

Ma’aikatan da ake zargi su ne Olusegun Babasola, Abisola Ahmed, Uchechukwu Uma, da Jude Aphaeus.

Ofishin EFCC
Ofishin EFCC Hoto: @officialefcc
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An taba kudin wasu kamfanoni

Kamar yadda PM News ta kawo rahoto, an saci kudin ne ta wasu katin ATM na kamfanoni biyar, har da American International Insurance Company Limited.

Sauran kamfanonin da aka sacewa kudi su ne: Interswitch; OVH Energy Marketing Ltd.; Fidelity Bank Sinking Fund Account sai kuma wani FSL Securities Ltd.

Wanda aka kawo ya bada shaida ya fadawa Alkali cewa bankin ne suka kawo masu korafi da kansu, nan take su kuma suka shiga binciken abin da ya faru.

Kara karanta wannan

A mutu ko ayi rai: Jerin taurari 6 da suka dauki makami, su na taya Ukraine yakin Rasha

Yadda aka yi abin

Nnaemeka Omewa shi ne lauyan da ya rika yi wa Peter tambayoyi, yana mai bada amsa a kotu.

Binciken ya nuna an yi wannan ta’adi ne ta hanyar amfani da manhajar bankin da ake kira Postillion App. Har ta kai aka gano cewa a Legas aka sace kudin.

A cewar Peter, sun gano cewa uku daga cikin ma’aikatan su na da hannu dumu-dumu a laifin, yayin da na hudun su yake ikirarin bai san abin da ya faru ba.

Mai bada shaidan ya nuna shaidan bidiyo, ya ce a cikin kudin aka aika N50m ga wani Omidiji Joseph Olanrewaju. Daga nan aka raba sauran zuwa wasu wurare.

Mutuwar auren Bill Gates

Watanni da mutuwar aurensu, Melinda French Gates ta karya azumin magana, ta tabo zamanta da Bill Gates da cin amanar da ya taba yi mata a shekarun baya.

A cewar Melinda French Gates, ta fara murmurewa daga abin da ya biyo baya, da farkon rabuwarta da Bill Gates, ta ce tayi kwana da kwanaki ta na kuka.

Kara karanta wannan

Yadda matan Gwamnoni su ka fusata mutane da suka kai wa Aisha Buhari ‘cake’ har Dubai

Asali: Legit.ng

Online view pixel