A karon farko, Melinda Gates ta fayyace abin da ya jawo rabuwarta da Attajiri Bill Gates

A karon farko, Melinda Gates ta fayyace abin da ya jawo rabuwarta da Attajiri Bill Gates

  • Melinda French Gates ta yi hira da ‘yan jarida a game da dalilin mutuwar aurenta da Bill Gates a 2021
  • Miss Melinda French Gates ta ce ba wani takamaimen abu daya ya jawo ta saki attajirin mijin na ta ba
  • A cewar ta, bayan shekaru 27 da aure, ta ji ba zai yiwu ta cigaba da zama a shimfida daya da Gates ba

United States - Melinda French Gates ta yi bayani a kan rabuwar ta da Billl Gates. Kusan wannan ne karon farko da aka ji wannan mata ta bude wannan babin.

A wata hira ta musamman da aka yi da ita a shirin CBS Morning kwana nan, Melinda French Gates ta ce ba a lokaci daya ta ji bukatar raba jiha da Bill Gates ba.

Melinda French Gates ta amsa tambaya a kan cin amanar ta da aka gano Bill Gates ya yi kusan shekaru 20 da suka wuce, ta ce tuni ta yafe wannan laifin na sa.

“Shakka babu, na yarda da yin afuwa, saboda haka ina tunanin mun ajiye wannan maganar.”

Ji nayi kawai da matsala - Melinda French Gates

“Ba wani takamaimen lokaci aka sami ko wani abu ne musamman ya auku ba. Kawai an zo wani lokaci da na ke ganin abin ya isa haka, na fahimci akwai matsala.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Sai ta kai ba zan iya yarda da abin da mu ka samu ba.” - Melinda French Gates.
Melinda Gates da Attajiri Bill Gates
Bill da Melinda Gates lokacin ana tare Hoto: www.marca.com
Asali: UGC

Marubuciyar kuma mai kokarin kare hakkin mata a Duniya ta fadawa ‘dan jaridar da ya yi hira da ita watau Gayle King cewa tayi kwanaki ta na rusa kuka a lokacin.

Bayan koke-koken da ta rika yi, Melinda ta ce akwai lokutan da ranta ya rika baci bayan sakin.

Melinda French Gates ta fara murmurewa

“Wannan yana cikin yanayi na alhini. Ka na alhinin rashin abin da ka ke tunani ka na da shi, abin da ka ke tunanin zai wanzu har ka bar Duniya.”
“Amma yanzu ina ji kamar an shiga wani sabon shafi. Yanzu mu na 2022 ne, cike nake da farin ciki, ina jiran abin da rayuwa tayi mani tanadi.”

- Melinda French Gates.

Yahoo ta rahoto cewa Shi ma Bill Gates mai shekara 66 ya bayyana cewa shekarar 2021 ta zo masa da wasu abubuwa marasa dadi, aurensa na shekara 27 ya watse.

Arzikin Bill Gates ya ragu

A 2021 ne aka ji cewa yanzu Melinda French Gates ta mallaki kimanin fam Dala $5.6b. Melinda ta samu wadannan kudi ne bayan ta rabu da mai gidanta, Bill Gates.

Rahotonni sun ce kudin da Bill Gates ya ba tsohuwar mai dakinsa a sakamakon mutuwar aurensu, ya sa ya sauka daga na hudu a jeringiyar Attajiran Duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel