A mutu ko ayi rai: Jerin taurari 6 da suka dauki makami, su na taya Ukraine yakin Rasha

A mutu ko ayi rai: Jerin taurari 6 da suka dauki makami, su na taya Ukraine yakin Rasha

  • Fitattun mutanen Ukraine da suka yi suna sun yin Allah-wadai da harin da Rasha ta kawo masu
  • Wasu su na bada gudumuwarsu ne a kafafen sada zumunta, amma wasu sun shiga har filin daga
  • Akwai ‘yan wasa da shahararrun ‘yan siyasan kasar Ukraine da yanzu ake wannan yakin da su

The National News ta kawo wasu shahararrun mutane, jarumai da taurarin da suke bada gudumuwarsu wajen yakar sojojin Rasha a cikin Ukraine.

Ga jerin nan kamar haka:

1. Oleksandr Usyk

Na farko a jerin shi ne babban ‘dan wasan damben Duniya kuma gwarzo Oleksandr Usyk. ‘Dan damben ya baro Landan, ya dawo kasarsa, ya sadaukar da ransa.

2. Petro Poroshenko

Tsohon shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko yana cikin wadanda aka gani rike da bindiga tare da sojoji. Poroshenko ne ya yi mulki kafin Volodymyr Zelenskyy.

Kara karanta wannan

Mun zo taya ku yakar Rasha: Dandazon 'yan Najeriya sun cika ofishin jakadancin Ukraine

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

3. Anastasia Lenna

Anastasia Lena wanda ta taba zama Sarauniyar kyau a Ukraine a shekarar 2015 ta na cikin wadanda ake yakin da su, Lena tana tare da dakaru a iyakokin kasarta.

Mutanen Ukraine
Masu taya kasarsu yakin Rasha Hoto: Daily Trust/Thenationalnews
Asali: UGC

4. Sergiy Stakhovsky

Ko da ya yi ritaya, har yanzu mutane za su iya tuna Sergiy Stakhovsky wanda ya yi suna wajen wasan tanis. Daily Trust ta ce yana cikin wadanda suke kare Ukraine.

5. Vaslily Lomachenko

Wani ‘dan damben Ukraine da yanzu yake filin daga shi ne Vaslily Lomachenko. ‘Dan wasan mai shekara 34 ya bar abin da yake yi a Girka, ya zo ya yaki sojojin Rasha.

6. Andriy Khlyvnyuk

Wani fitaccen mutumin da aka ji labarin ya shiga yakin Rasha da Ukraine shi ne Andriy Khlyvnyuk. Mawakin ya yi damara, yana kare kasarsa daga Rashawa.

Ukraine za ta shiga EU?

Kara karanta wannan

Ana tsakiyar yaki da Rasha, kasar Ukraine ta nemi shiga cikin kungiyar tarayyar Turai

Mai girma shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya sa hannu domin su shiga kungiyar EU. An yi wannan ne a lokacin da kasar ke kokarin yin sulhu da Rasha.

Wani hadimin shugaban kasar, Sergii Nykyforov ya bada wannan sanarwa a shafinsa na Facebook a makon nan. Ana sa rai takardun Ukraine sun isa Brussels.

Asali: Legit.ng

Online view pixel