Minista ya yi wa daliban jami’a albishir, 'ASUU ta kusa janye yajin-aikin da ta shiga'

Minista ya yi wa daliban jami’a albishir, 'ASUU ta kusa janye yajin-aikin da ta shiga'

  • Dr. Chris Ngige ya bayyana inda aka kwana a game da tattaunawar gwamnati da wakilan ASUU
  • Ministan kwadago da samar da ayyukan yana ganin yajin-aikin ASUU ya na daf da zuwa karshe
  • Idan abubuwa sun tafi yadda aka so, ba dole ba ne ASUU ta dauki har wata guda ta na yajin-aikin

Abuja - Ministan kwadago da samar da ayyukan yi a kasa, Chris Ngige ya na sa ran kungiyar ASUU ba za ta shafe tsawon wata guda ta na yajin-aiki ba.

Jaridar PM News ta rahoto Dr. Chris Ngige yana yi wa manema labarai wannan bayani bayan ya tashi daga wani taro da ya yi da shugabannin ASUU a Abuja.

Dr. Chris Ngige ya ce sun cin ma matsaya a kan wasu abubuwa da-dama, kuma an tsaida lokacin da za a aiwatar da alkawuran da gwamnati tayi wa kungiyar.

Kara karanta wannan

Sanusi II: Abu 1 da ya sa Jonathan da Ganduje suka tsige ni daga CBN da sarautar Kano

A cewar Ministan tarayyar, wakilan ASUU sun yarda su tuntubi ‘ya ‘yansu domin jin ta bakinsu, idan sun amince da tayin da aka yi masu, za su koma kan aiki.

Kamar yadda The Guardian ta rahoto a ranar Laraba, Ministan ya ce an yi magana kan yarjejeniyar MoA da aka sa wa hannu kafin a koma aiki a 2020.

Shugabannin ASUU
Wakilan ASUU a Majalisar Tarayya Hoto: africannewstoday.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Albashin malaman jami'a

“Abubuwa daya zuwa biyu suka rage mana. Daga cikin sababbin abubuwan shi ne jin batun halin da ma’aikata suke ciki.”
An yi yarjejeniya a 2009 duk bayan shekaru biyar za a duba halin da ma’aikata suke ciki. Tun 2014 aka yi na karshe.” - Ngife,

Ngige ya yi bayanin abin da ya kawo cikas wajen cika wannan alkawari, amma ya bayyana cewa an kafa wani sabon kwamiti da zai yi aiki a kan maganar albashi.

Kara karanta wannan

Ana kokarin biyawa ASUU bukatunta, Minista ya fadi kudin da aka ba Malaman jami’a

Amma Ministan ya gargadi malaman jami’ar cewa ba za su kawo abin da ya sabawa tsarin NSIWC ba, wanda ita ce hukumar da ke tsaida albashin ma’aikata.

Za a bude jami'o'i?

Legit.ng Hausa ta na da labari cewa kungiyar ASUU ta reshen jami’ar Bayero da ke Kano ta ce ka da a janye yajin-aikin sai an cika duka alkawuran da aka yi a 2020.

Akwai alamun cewa yajin-aikin zai iya wuce yadda Ministan yake tunani. Wani malami a ABU Zaria ya ce idan ba su gani a kasa ba, ba za a bude dakunan karatu ba.

Mun biya ASUU N92bn - Minista

Idan ba a manta ba, Ministan kwadago na tarayya, Chris Ngige ya zauna da Muhammadu Buhari a kan yajin-aikin jan kunnen da malaman jami'ar kasar nan suka shiga.

Dr. Chris Ngige ya ce daga karshen 2020 zuwa yanzu, gwamnati ta biya ‘Yan ASUU fiye da N90bn.

Kara karanta wannan

Yajin aiki a Jami'o'i: Abubuwan da aka tattauna tsakanin ASUU da FG a taron yau Talata

Asali: Legit.ng

Online view pixel