Ministan Buhari Ta Bukaci Ƴan Najeriya Su Yi Wa Waɗanda Suka Kashe Dokar Bawa Mata Muƙamai Na Musamman Addu’a

Ministan Buhari Ta Bukaci Ƴan Najeriya Su Yi Wa Waɗanda Suka Kashe Dokar Bawa Mata Muƙamai Na Musamman Addu’a

  • Ministar harkokin mata, Pauline Tallen ta ce mazan da suka kashe dokar da zata samar wa mata matsayi na musamman suna bukatar addu’a
  • An samu bayanai akan yadda majalisar tarayya ta nuna kin amincewar ta akan kudirin yayin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya
  • Ministar ta kwatanta rashin amincewar majalisar a matsayin abu mafi muni kuma abin kunya wanda tace sam bai dace ba kuma mata baza su hakura ba

FCT, Abuja - Mrs Pauline Tallen, Ministar Harkokin Mata a Najeriya ta ce mazan da suka kashe dokar sama wa mata matsayi na musamman suna bukatar addu’a.

Daily Trust ta ruwaito yadda majalisar tarayya ta nuna rashin amincewar ta akan dokar yayin da ake gyare-gyare a kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Mata sun tare kofar majalisa saboda kin amincewa da wani kudirin mata

Ministan Buhari Ta Bukaci Ƴan Najeriya Su Yi Wa Waɗanda Suka Kashe Dokar Bawa Mata Muƙamai Na Musamman Addu’a
Ministan MataTa Bukaci Ƴan Najeriya Su Yi Wa Waɗanda Suka Kashe Dokar Bawa Mata Muƙamai Na Musamman Addu’a. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta furta hakan ne yayin tattaunawa da manema labaran cikin gidan gwamnati akan yadda taron kwamitin zartarwa ta tarayya, FEC ya kare akan batun gyaran dokar jinsi ta kasa ta 2021-2026, Daily Trust ta ruwaito.

Mazan da suka ki yarda da dokar suna bukatar addu’a

A ranar Talata, ‘yan majalisar tarayyar suka nuna rashin amincewar su akan yarda a samar wa mata kujeru kashi 35% na kujerun majalisar tarayya da na jihohi, ta hanyar gyara akan kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Ministar ta kwatanta rashin amincewar tasu a matsayin abu mafi muni da ban kunya wanda majalisar da maza suka yawaita ta yi.

Ta yi ikirarin jan hankalin mata akan sama wa kansu mafita a zaben 2023 da ke karatowa.

Kamar yadda ta ce:

“Muna ta shirye-shirye da matan da ke majalisar tarayya. Kuma ina mai tabbatar muku da cewa matan Najeriya baza su tsaya haka nan ba har sai sun samu nasara.

Kara karanta wannan

Yajin aiki a Jami'o'i: Abubuwan da aka tattauna tsakanin ASUU da FG a taron yau Talata

“Akwai wasu abubuwa da muke shiryawa amma ba za mu bayyana ba. Duk shirye-shiryen mu na zaben 2023 ne. Kuma da yardar Ubangiji sai mun samu nasara.”

Pauline Ta ce akwai matakin da suke shirin dauka amma ba za ta bayyana ba

Yayin da aka tambayeta akan shirin nata ko na kin zaben maza ne a 2023, cewa tayi:

“Mun yarda da demokradiyya, kuma mun yarda da cewa kowa yana da damar da zai gwada ficen da ya yi ta hanyar tsayawa takara. Amma idan zaku yarda, mata da matasa su ne suka fi kowa zabe.
“Idan ka share wadanda su ne suka fi kowa zabe tabbas sai wani abu ya faru.”

Ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi wa wadanda suka kashe dokar addu’o’i don suna bukatar hakan.

Ta yi amfani da damar wurin godiya ga Buhari akan taya mata murnar ranar su da ya yi

Tallen ta ce adalci shi ne kudirin da ake fatan tabbatarwa zuwa 2023 wanda zai ba kowa damar a dama da shi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Majalisa ta yi watsi da kudurin kirkiro wa mata Kujeru na musamman, da kudirin VAT

Kamar yadda ta ce, shugaban kasa ya yi iyakar kokarinsa na sanya mata cikin harkar shugabanci.

Amma a cewarta, lokaci ya yi da mata zasu mike tsaye wurin samar wa kansu hakki don sanya hannu wurin ci gaban kasa.

Ta yi amfani da damar wurin mika godiyar ta ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya taya mata murnar zagayowar ranar su ta kasa da kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel