Ministan Kuɗi: Najeriya Bata Yi Amfani Da Kuɗaɗen Tallafin Da Aka Bata Ta Hanyoyin Da Suka Dace Ba

Ministan Kuɗi: Najeriya Bata Yi Amfani Da Kuɗaɗen Tallafin Da Aka Bata Ta Hanyoyin Da Suka Dace Ba

  • Zainab Ahmed, Ministan Kudi, Kasafin Kudi da Tsarin Kasa ta bayyana cewa Najeriya bata yi amfani da kudaden da aka bata ta hanyar da suka dace
  • Ministan ta bayyana hakan ne yayin wani taron bita da ma'aikatar ta ta shirya wa 'yan Majalisar Tarayyar Najeriya a Legas don tattaunawa kan tattalin arziki
  • Zainab ta ce idan aka kwatanta Najeriya da sauran kasashe da suke samun tallafi da bashi daga hukumomi kamar bankin duniya da Afirka, Najeriya tana baya

Jihar Legas - Ministan Kudi, Kasafin Kudi da Tsarin Kasa ta Najeriya, Mrs Zainab Ahmed ta ce Najeriya ba ta amfani da kudaden da aka bata tallafi domin yin ayyukan gina kasa da cigabanta, rahoton Daily Trust.

Ta bayyana hakan ne a ranar Talata a wurin taron bita da ma'aikatarta ta shirya wa mambobin Majalisar Tarayya da aka yi a Legas kan yadda za a inganta amfani da kudaden da ake tallafawa Najeriya don aiki.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Ministan Kuɗi: Najeriya Bata Yi Amfani Da Kudaden Da Aka Bata Tallafi Ta Hanyoyin Da Suka Dace Ba
Najeriya Bata Yi Amfani Da Kudaden Da Aka Bata Tallafi Ta Hanyoyin Da Suka Dace Ba, Ministan Kuɗi
Asali: Twitter

Ta lura cewa daya daga cikin muhimman hanyar da ake samun kudade domin yin muhimman ayyuka shine daga tallafi, musamman daga hukumomi kamar Bankin Duniya da Bankin Cigaban Afirka.

A cewarta:

"Idan ba a yi amfani da kudin da aka ranto ta hanyar da suka dace ba, cigaba da bunkasa kasa na samun tangarda."

Najeriya tana baya a bangaren aiwatar da ayyukan da suka dace da kudaden tallafi da bashi, Zainab

"Najeriya tana baya a bangaren aiwatar da ayyukan cigaba idan aka kwatanta da sauran kasashe da Bankin Duniya ta ke bawa tallafi.
"Kowa ya san yadda ake nuna damuwa kan karuwar bashin kasashen waje a kasa. Hakan ya matsa wa gwamnati ta tabbatar ana amfani da kudaden ta hanyoyin da suka dace don inganta tattalin arziki," in ji Ministar.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: 'Yan Najeriya sun samu mafaka a kasashe biyu da ke makwabtaka da Ukraine

Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin N64,684 bisa basukan da ƙasar ta ci a ƙasashen waje

A wani labarin, kun ji cewa bisa yawan ‘yan Najeriya da kuma yawan basukan da ake bin ta, kowa ya na da N64,684 a kan sa.

Kamar yadda kowa ya san yawan bashin da Najeriya take ta amsowa daga kasashen ketare, yanzu ko wanne dan Najeriya ya na da bashin $157 ko kuma N64,684 a kan sa.

Bisa wannan kiyasin, masanin tattalin arzikin kasa, Dr. Tayo Bello ya bayyana damuwar sa akai inda ya ce duk da zuzurutun basukan, babu wasu abubuwan ci gaba da aka samar wadanda za su taimaka wurin biyan basukan kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel