Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin N64,684 bisa basukan da ƙasar ta ci a ƙasashen waje
- Sakamakon bashin da Najeriya take ta narkowa daga kasashen waje ko wanne dan Najeriya ya na da bashi a kan sa
- Kamar yadda aka kirga yawan ‘yan Najeriya, an gano cewa ana bin ko wanne dan Najeriya $157 ko N64,684
- Sai dai Dr. Tayo Bello, masanin tattalin arzikin kasa ya ce babu wani abin a zo a gani da a ka yi da basukan
Bisa yawan ‘yan Najeriya da kuma yawan basukan da ake bin ta, kowa ya na da N64,684 a kan sa.
Kamar yadda kowa ya san yawan bashin da Najeriya take ta amsowa daga kasashen ketare, yanzu ko wanne dan Najeriya ya na da bashin $157 ko kuma N64,684 a kan sa.
Bisa wannan kiyasin, masanin tattalin arzikin kasa, Dr. Tayo Bello ya bayyana damuwar sa akai inda ya ce duk da zuzurutun basukan, babu wasu abubuwan ci gaba da aka samar wadanda za su taimaka wurin biyan basukan kamar yadda Leadership ta ruwaito.
A ranar 30 ga watan Yunin 2021, kamar yadda ofishin tattalin basuka ya bayyana, ana bin Najeriya bashin $33.468 biliyan.
A ranar 9 ga watan Oktoban 2021, bisa kidayar da majalisar dinkin duniya ta yi, yawan ‘yan Najeriya ya kai 212,599,044 kuma idan an raba wa ko wannen su bashin da ake bin Najeriya, kowa zai biya $157.42 ko N64,684.
A haka kasar take tunanin kara ranto naira tiriliyan 6 don cikasa kasafin naira tiriliyan 16 da za ayi amfani da shi don kasafin kudin amfanin shekara mai zuwa.
Tsakanin watan Janairu zuwa na Yunin 2021, kudaden da Najeriya take ranta ya karu zuwa $120.74 biliyan.
Kamar yadda Dr. Bello ya ce bisa ruwayar Leadership:
“Matsalar Najeriya shi ne yadda kudaden harajin da take samu ba sa dacewa da kudaden da take kashewa kuma bashin da take ci ba ya nunawa ta hanyar bunkasa kasa da kuma kawo wata hanyar samar da kudade ta daban.”
Bello ya zargi wasu mutane da wawurar kudaden kasa
Ya zargi mutane da sace kudaden da ake rantowa sannan ya bayyana damuwar sa akan yadda ake dankara kudaden bashin don yin titin jirgin kasan da zai kai kasar Nijar saboda ‘yan kasar Nijar ‘yan uwan Buhari ne.
Ya kara da cewa:
“Matsalar cin bashin kasashen ketare shi ne idan za a biya da daloli za a biya har da riba banda gundarin kudin. Sannan akwai matsala akan rantar kudade don biyan albashi.”
A ranar 31 ga watan Disamban 2020, kudaden da kasashen ketare su ke bin Najeriya sun kai $33.348 biliyan amma zuwa karshen watan Yuni sun karu zuwa $33.468 biliyan.
Yanzu haka akwai tarin basuka da kungiyar cigaban kasa da kasa ta IDA ta Bankin duniya take bin Najeriya. Tana bin Najeriya $11.62 biliyan banda wasu basukan na daban.
Najeriya tana rike da bashin $3.4 biliyan ta IMF da kuma $3.48 biliyan na bankin China na EXIM.
Ministar kudi, kasafi da tsarin kasa, Mrs Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a wani taro da su ka yi ranar Juma’ar da ta gabata a Abuja don bayyana kasafin 2022.
A cewar ta, a watanni 7 na farkon shekarar nan, gabadaya kudaden amfanin gwamnati sun kai N8.14 tiriliyan.
Kamar yadda ta ce:
“Don haka ne muke sa ran gwamnatin tarayya za ta daure ko wanne bashi ga abin amfanin da aka yi da shi, sakamakon yadda duk basukan Sukuk da aka dauka a ka yi amfani da su wurin yin ayyukan bunkasa kasa.”
Asali: Legit.ng