Kano: Ganduje Ya Naɗa Ɗangote, Ɗantata Da AbdusSamad Muƙami a Hukumar Zakka

Kano: Ganduje Ya Naɗa Ɗangote, Ɗantata Da AbdusSamad Muƙami a Hukumar Zakka

  • Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya nada mai kudin nahiyar Afirka, Aliko Dangote, kawun sa Aminu Dantata da Abdulsamad Rabi’u a matsayin mambobin hukumar zakkar jihar
  • An samu wannan bayanin ne a wata takarda wacce kwamishinan labarai, Muhammad Garba, ya saki inda ya sanar da sauran mambobin hukumar
  • Wannan ci gaban ya biyo bayan yadda kwamitin zartarwa ta Jihar Kano ta sake kafa hukumar Zakka da Hubsi inda Ibrahim Mu’azzam Maibushra ya ke shugabanta

Kano - A ranar Laraba gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya nada mai kudin Afirka, Aliko Dangote, kawun sa, Aminu Dantata da Abdulsamad Rabi’u a matsayin mambobin hukumar Zakka da Hubsi na jihar.

An samu labarin nan ne a wata takarda wacce kwamishinan labaran jihar, Muhammad Garba ya saki, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abin da PDP za tayi kafin tayi nasara a zabe - Gwamna Tambuwal ya bada lakanin 2023

Kano: Ganduje Ya Naɗa Ɗangote, Ɗantata Da AbdusSamad Muƙami a Hukumar Zakka
Kano: Ganduje ya nada Dantata, Dangote da AbdusSamad a matsayin mambobin hukumar zakka. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran mambobin kungiyar sun hada da AbdulMutallab Ahmed a matsayin kwamishina I, Dr Lawi Sheikh Atiq a matsayin kwamishina na II na hukumar.

Wannan ci gaban ya biyo bayan sake kafa hukumar da kwamitin zartarwa ta jihar ta yi wa hukumar Zakka da Hubsi inda Ibrahim Mu’azzam Muibushira yake shugabanta, kamar yadda Daily Nigerian ta nuna.

Akwai wasu mambobin hukumar

Akwai sauran mambobi wadanda suka hada da wakilan masarautu biyar da ke jihar, wakilan ma’aikatar labarai, na ma’aikatar harkokin addini, tare da na kasuwannanin Kurmi, Rimi, Kwari da Singer.

Kwamishinan ya sanar da cewa hukumar ta amince da kafa kwamitin tantancewa da hukumomin addini na kasa da kasa.

Farfesa Sani Zaharaddeen, babban limamin Jihar Kano, wanda zai zama shugaba, Dr Muhammad Adamu, kwamishinan harkokin addini a matsayin mataimakin shugaban tare da Auwalu Yakasai a matsayin sakatare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel