Boko Haram: Hotunan iyalan 'yan canji da aka kama yayin da suka fito zanga-zanga a Kano

Boko Haram: Hotunan iyalan 'yan canji da aka kama yayin da suka fito zanga-zanga a Kano

  • Iyalan 'yan canjin Kano da aka kama da alaka da ta'addancin Boko Haram sun fito zanga-zanga kan titunan birnin
  • Cike da alhini tare da bacin rai, sun bayyana sanye da kayan makaranta inda kananan yara ke kokawa kan rashin ganin mahaifansu
  • Kamar yadda ta faru, watanni 11 da suka gabata gwamnati ta kwamushe 'yan canjin kan zargin tura wa 'yan Boko Haram kudi

Kano - Fusatattun iyalan 'yan canji da aka kama kan zargin suna da alaka da ta'addanci sun fito titunan jihar Kano a safiyar Laraba domin yin zanga-zangar lumana.

Daily Trust ta ruwaito cewa, 'yan canjin da aka kama watanni 11 da suka gabata, sun kasance a garkame kan zarginsu da ake da turawa 'yan ta'addan Boko haram kudi.

A watan da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta amincewa iyalansu da su gana da su, karon farko tun bayan kama su da aka yi.

Kara karanta wannan

Abba Kyari: Ji nake kamar nayi kuka idan dan sanda ya aikata laifi, IGP Alkali Baba

Ga jerin hotunansu:

Boko Haram: Hotunan iyalan 'yan canji da aka kama yayin da suka fito zanga-zanga a Kano
Boko Haram: Hotunan iyalan 'yan canji da aka kama yayin da suka fito zanga-zanga a Kano. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ku sakan mana mazajenmu, Iyalan yan BDC da ake zargi da turawa yan Boko Haram kudi a Kano

A wani labari na daban, iyalan yan kasuwar canji 45 a jihar Kano da aka damke watanni 11 da suka gabata sun yi kira ga gwamnati ta sakin musu mazajensu ko kuma ta gurfanar da su a kotu.

Iyalan wanda suka hada da mata da yara sun kai kuka fadar mai martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ranar Alhamis, 4 ga watan Febrairu, 2022, rahoton Daily Trust.

Sun bayyana cewa rashin mazajensu da iyayen yaransu ya jefasu cikin mumunan hali.

Bayan sauraron korafinsu, Sarkin Kano ya bukaci mutum biyar cikin matan su rubuta korafinsu a takarda kuma yayi alkawarin daukan mataki.

Kara karanta wannan

Niger: 'Yan ta'adda sun ragargaza garinsu sakataren gwamnatin jihar

Asali: Legit.ng

Online view pixel