Ku sakan mana mazajenmu, Iyalan yan BDC da ake zargi da turawa yan Boko Haram kudi a Kano

Ku sakan mana mazajenmu, Iyalan yan BDC da ake zargi da turawa yan Boko Haram kudi a Kano

  • Mata, yara da iyayen mutum 45 da gwamnatin tarayya ta damke a jihar Kano sun kai kuka wajen Sarkin Kano
  • Kimanin shekara daya yanzu, an damke yan kasuwan canjin da ake zargin sun taimaka wajen turawa yan Boko Haram kudi
  • Ministan Labarai a jiya Laraba ya ce za'a gurfanar da su a kotu nan ba da dadewa ba

Kano - Iyalan yan kasuwar canji 45 a jihar Kano da aka damke watanni 11 da suka gabata sun yi kira ga gwamnati ta sakin musu mazajensu ko kuma ta gurfanar da su a kotu.

Iyalan wanda suka hada da mata da yara sun kai kuka fadar mai martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ranar Alhamis, 4 ga watan Febrairu, 2022, rahoton Daily Trust.

Sun bayyana cewa rashin mazajensu da iyayen yaransu ya jefasu cikin mumunan hali.

Kara karanta wannan

An kashe jami’an yan sanda uku, an sace mazauna da dama yayin da yan bindiga suka kai hari a Neja

Bayan sauraron korafinsu, Sarkin Kano ya bukaci mutum biyar cikin matan su rubuta korafinsu a takarda kuma yayi alkawarin daukan mataki.

Zaku tuna cewa an damke wani yan kasuwan canji da zargin taimakawa wajen turawa yan ta'addan Boko Haram kudi.

Daga cikin yan kasuwan canji 45 da aka damke akwai Baba Usaini, Abubakar Yellow (Amfani), Yusuf Ali Yusuf (Babangida), Ibrahim Shani, Auwal Fagge da Muhammad Lawan Sani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Boko Haram kudi
Ku sakin mana mazajenmu, Iyalan wadanda ake zargi da turawa yan Boko Haram kudi Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Jawabin matan da suka kai kuka wajen Sarki

Daily Trust tace ta samu ji daga bakin wasu daga cikin iyalan.

Halima Jibrin Garo, wacce tace an damke mijinta tace:

"'Yayanmu sun daina zuwa makaranta saboda rashin kudi. Abinci ya zama mana matsala. Wadanda ke taimakonmu sun gaji."

Zannira Uwaisu, matar Auwalu Ali Alhassan tace an kama mijinta tare da 'yan uwansa guda uku.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta baiwa iyalan yan sanda bakwai da aka kashe milyan 7

"Uwar mijina na kwance yanzu sakamakon kama yayanta hudu. Kishiyata ma na kwance, yaranta 9. Su kawo mana dauki. Yayanmu 16 na nan tare da mu; muna wahala. Sun daina zuwa makaranta."

Mun gano masu daukar nauyin yan ta'addan Boko Haram guda 96, Lai

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa hukumar leken asirin kudade a Najeriya NFIU ta gano mutum 96 masu baiwa yan ta'adda kudi, musamman yan Boko Haram da ISWAP.

Gwamnati ta kara da cewa NFIU ta bankado mutum 424 dake aiki tare da masu daukar nauyin, kamfanoni 123 da kuma yan kasuwan canji 33.

Lai Mohammed yace:

"Binciken ya taimaka wajen damke mutum 45 wadanda za'a gurfanar ba da dadewa ba kuma a kwace dukiyoyinsu."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel