Abba Kyari: Ji nake kamar nayi kuka idan dan sanda ya aikata laifi, IGP Alkali Baba

Abba Kyari: Ji nake kamar nayi kuka idan dan sanda ya aikata laifi, IGP Alkali Baba

  • IGP na yan sandan ya gargadi jami'an yan sanda bisa tare hanyoyin da suke yi don amsan kudi hannun direbobi
  • Alkali ya yi kira ga jami'ansa suyi aiki da tsoron Allah duk inda aka turasu saboda bai jin dadi idan aka kama dan sanda ya aikata laifi
  • Wannan ya biyo bayan damke DCP Abba Kyari, wanda aka dakatar kuma aka kama dumu-dumu a harkallar kwayoyi

Abuja - Sifeto Janar na yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, a ranar Talata ya bayyana bacin ransa bisa yadda ake aikata laifuka a fadin kasa.

IGP, wanda da alamun yana magana ne kan lamarin jami'an dan sandan da aka dakatar Abba Kyari, ya bayyana hakan yayin ziyarar kwana guda da ya kai hedkwatar yan sandan Abuja, rahoton TheNation.

Yace:

"Muyi abinda ya dace a lokacin da ya dace. Ji nake kamar nayi kuka idan aka kama yan sanda da aikata laifuka."

Kara karanta wannan

Wani bawan Allah ya daba wa dan Acaba makami har lahira kan ya buge masa Kare a Gombe

IGP Alkali Baba
Abba Kyari: Ji nake kamar nayi kuka idan dan sanda laifi ya aikata laifi, IGP Alkali Baba Hoto: NPF
Asali: Facebook

IGP ya yi kira ga yan sandan su daina amfani da karfin bindiga wajen tsanantawa jama'a.

Ya yi kira garesu suji tsoron Allah yayin gudanar da ayyukansu.

Yace:

"Kuyi ayyukanku da tsoron Allah. Ku daina kai hari domin kama mutum ba bisa tsari ba. Ku daina tare hanya don tsanantawa mutane don samun kudi."

Alkali ya karkare jawabin da kira ga yan sandan su karanta sabuwar dokar zaben da Shugaba Buhari ya rattafa hannu don fahimtar dokar.

IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda jami’an ‘yan sanda ke amfani da bindigogi ba ta hanyoyin da basu dace ba a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Ya bukaci jami’an ‘yan sanda da kada su yi amfani da ikonsu ta hanyar sanya rayuwar 'yan Najeriya cikin wahala ba gaira ba dalili.

IGP din ya kuma shawarci hukumomin tsaro da su rungumi hadin kai domin samun sakamako mai kyau a yaki da miyagun laifuka a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel