Kotu ta bai wa NDLEA muhimmin umarni kan kula da lafiyar Abba Kyari

Kotu ta bai wa NDLEA muhimmin umarni kan kula da lafiyar Abba Kyari

  • Babbar kotun tarayya dake Abuja ta umarci NDLEA da ta bai wa DCP Abba Kyari damar kula da lafiyar sa yayin da yake tsare
  • Alkali Inyang Ekwo ne yayi umarni da hakan a ranar Litinin, yayin kafa sharudda a kan bukatar bada belin da Kyari ya shigar
  • Sai dai lauyan hukumar NDLEA, Joseph Sunday ya ce, NDLEA tana da isashshen ilimin kula da lafiyar mai korafin

FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya (FHC) ta Abuja ta umarci hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) da ta bar dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sandan da aka kama(DCP) Abba Kyari ya samu damar kula da lafiyar sa.

Alkali Inyang Ekwo yayi umarni da hakan ne a ranar Litinin, yayin kafa sharudda a kan bukatar bada belin da Kyari ya shigar, tsohon kwamandan hukumar hadin gwuiwar binciken sirri (IRT) na 'yan sandan Najeriya (NPF), The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta yi watsi da bukatar Abba Kyari, ta ce ba za a bada belinsa ba

Da duminsa: Kotu ta bai wa NDLEA muhimmin umarni kan lafiyar Abba Kyari
Da duminsa: Kotu ta bai wa NDLEA muhimmin umarni kan lafiyar Abba Kyari. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Alkali Ekwo ya ce, bukatar bada belin Kyari ya sha gaban umarnin da Alkaliyar wannan babbar kotun tarayyar ta Abuja, Mai shari'a Zainab Abubakar, ta bawa NDLEA izinin tsare jami'in dan sandan na tsawon kwana 14 da farko.

The Nation ta ruwaito cewa, alkalin ya ce, tunda kotu ta yanke hukuncin umarni a kan cigaba da tsare Kyari, ba shi da hurumin canza hakan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Umarnin da kawai zan iya badawa akan abunda na fada shi ne, hukumar za ta bai wa wanda ke tsaren damar neman lafiyar sa, yayin da yake tsare," a cewar Alkali Ekwo.

Da haka ne, Alkalin ya dage sauraran karar zuwa 15 ga watan Mayu, don sauraron karar da ya shigar na hakkokinshi na dan kasa, wanda daga ciki ne yake kalubalantar tsare shi da kuma san a biya shi diyya.

Kara karanta wannan

Alkali ya bada umarni hukumar EFCC ta karbe gidan tsohon Gwamnan APC a Abuja

Lauyan wanda ake tuhumar, Cynthia Ikena, yayin zaman kotu a kan shigar da bukatar bada belin, tayi ikirarin cewa wanda take karewar yana fama da hawan jini da ciwon siga, hakan na nuna bukatar kula da magungunan shi da abincin shi.

Ms. Ikena Alos ta yi ikirarin cewa, an hana ta ganin Kyari a ranar Alhamis, lokacin da tayi kokarin ganin shi yayin da yake tsere a hannun NDLEA.

Ta kara da cewa, wanda take karewan ba ya samun abinci mai kyau tun lokacin da aka kama shi a ranar Juma'a, 12 ga watan Fabrairun wannan shekarar duk da matsalar lafiyar da yake fama dashi.

Yayin mayar da martani, lauyan NDLEA Joseph Sunday, ya bayyana wa kotun muhimmancin cigaba da tsare Kyari, don gudun kada ya shiga hurumin binciken da ake cigaba da yi.

Sunday ya ce, duk da hukumar ta gama bincike a kan abunda ya shafi sabgar miyagun kwayoyin, amma tana cigaba da binciken Kyari akan batun kudin damfara.

Kara karanta wannan

Harkallar kwaya: Kotu a Abuja ta ce NDLEA ta duba bukatar belin Abba Kyari cikin awa 48

Game da ikirarin rashin lafiyar Kyari, Sunday ya bayyana yadda hukumar ke da isashshen ilimin kula da lafiyar mai korafin (Kyari).

NDLEA ta cafke kudi har $4.7 na jabu a Abuja, ta yi ram da maijego dauke da kwayoyi

A wani labari na daban, hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta kama wasu kudin jabu a tsabarsu da suka kai $4.7 miliyan a Abuja.

A wata takarda da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya ce jami'an hukumar a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 18 ga watan Fabrairu sun tsare wasu kaya da aka aiko daga Legas zuwa Abuja a yankin Abaji da ke babban birnin tarayya.

Kamar yadda Babafemi yace, kama kudin jabun ya yi sanadin da aka damke babban wanda ake zargi mai shekaru 52 mai suna Abdulmumini Maikasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel