Ganduje: Hukuncin Kisa Ko Daurin Rai Da Rai Za a Zartar Wa Makiyaya Masu Tada Rikici a Kano

Ganduje: Hukuncin Kisa Ko Daurin Rai Da Rai Za a Zartar Wa Makiyaya Masu Tada Rikici a Kano

  • Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Jihar Kano ya gargadi makiyaya game da satar shanu da garkuwa da hare-hare
  • Ganduje ya ce duk wani makiyayi da aka samu da aikata laifin zai fuskanci hukuncin kisa ko kuma daurin rai da rai
  • Gwamnan ya yi wannan jawabin ne wurin wani taron kaddamar da yi wa shanu da dabobi rigakafi a jihar Kano

Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya gargadi makiyaya su guji aikata laifuka ko kuma su fuskanci hukuncin kisa ko daurin rai da rai, rahon Daily Trust.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da ya ke kaddamar da shirin yi wa dabobi rigakafi a Kadawa, karamar hukumar Garun Mallam.

Ganduje: Hukuncin Kisa Ko Daurin Rai Da Rai Za a Zartar Wa Makiyaya Masu Tada Rikici a Kano
Ganduje: Hukuncin Kisa Ko Daurin Rai Da Rai Za a Zartar Wa Duk Makiyaya Da Aka Kama Da Laifin Tada Rikici. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Ganduje ya ce jiharsa ta tanadi hukuncin kisa ko daurin rai da rai ga makiyaya masu kai hari

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Faɗa Wa Rasha Ta Janye Sojojinta Daga Ukraine

Ganduje ya ce a maimakon su yi rikici, ya kamata su rungumi tsarin kiwo na zamani su inganta tattalin arzikinsu tare da dogaro da kai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Na yi farin cikin ganin muna zaune lafiya a nan ba tare da rikicin makiyaya da manoma ba a Kano. Don haka, ina shawartar ku da ku guji aikata laifi ku rungumi kiwo. Muna da doka a Kano kuma duk wanda aka kama yana satar shanu ko dan bindiga, zai fuskanci daurin rai da rai ko hukuncin kisa," in ji Ganduje.

A cewar Ganduje, jiharsa na fatan yi wa shanu miliyan daya rigakafi a shekarar 2022 domin inganta kiwo a jihar.

Ya ce gwamnatin jihar ta dauki ma'aikata lafiya guda 220 da za su yi aiki tare da makiyayan domin bunkasa kiwonsu da tattalin arziki.

Ganduje ya ce nasarar da aka samu a bara ya janyo cigaba sosai a bangaren kiwon don haka akwai bukatar a kara rubanya nasarorin, yana mai cewa kiwo na cikin abubuwan da gwamnatin tarayya ta mayar da hankali a kai.

Kara karanta wannan

Rayuwar aure: Yadda wata kotu ta gimtse auren da yayi shekaru 7 saboda sabani tsakanin ma'aurata

Kano: An cafke mai wankin mota da ya tsere da motar kwastoma ta N8.5m zuwa Katsina

A wani labarin, an kama wani mai aiki a wurin wankin mota a Kano, Abdullahi Sabo, saboda tsere wa da motar kwastoma da aka kawo masa wanki, Premium Times ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Daura, Jihar Katsina da motar na sata.

Mr Kiyawa ya ce, a ranar 30 ga watan Nuwamba, yan sanda sun samu korafi daga wata mazauniyar Badawa Quaters a Kano inda ta ce wani mai aiki a wurin wankin mota ya gudu masa da motarsa Honda Accord ta shekarar 2017.

Asali: Legit.ng

Online view pixel