A Yayin Da ASUU Ke Yajin Aiki, Kungiyoyin SSANU Da NASU Suna Barazanar Tafiya Yajin Aiki

A Yayin Da ASUU Ke Yajin Aiki, Kungiyoyin SSANU Da NASU Suna Barazanar Tafiya Yajin Aiki

  • Jami’o’in Najeriya suna shirin fuskantar yajin aiki yayin da kungiyoyin ma’aikata marasa koyarwa suke barazanar nuna wa gwamnatin tarayya gazawar ta
  • Kungiyar hadin gwiwar kungiyoyin guda biyu, JAC ta bayar da sanarwa akan shirin ta na tafiya yajin aiki a taron da ta yi a Abuja ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairun 2022
  • Kungiyoyin guda biyu su ne kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya, SSANU da kungiyar ma’aikatan jami’o’i marasa koyarwa, NASU inda suka nuna rashin jin dadin su akan yadda gwamnati ta ki cika alkawura

Abuja - Jami’o’in Najeriya suna gab da fara fuskatantar yajin aiki yayin da kungiyar hadin gwiwa ta ma’aikatan jami’o’i marasa koyarwa suke yi wa gwamnatin tarayya barazanar tafiya yajin aiki matsawar ba a cika musu bukatun su ba, The Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gombe: Dan Majalisa Ya Fice Daga APC, Ya Ce Wasu Mambobin Za Su Bi Sahunsa

Kwamitin hadin gwiwa, JAC, wanda kungiyoyin guda biyu ke karkashin inuwar ta, ta yi barazanar ne bayan kammala taron shugabannin JAC wanda suka yi a ranar Alhamis 24 ga watan Fabrairun 2022 a Abuja.

A Yayin Da ASUU Ke Yajin Aiki, Kungiyoyin SSANU Da NASU Suna Barazanar Tafiya Yajin Aiki
Kungiyoyin SSANU Da NASU Suna Barazanar Tafiya Yajin Aiki. Hoto: The Sun
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyoyin guda biyu sune kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya, SSANU da kungiyar ma’aikata marasa koyarwa, NASU wanda taron ya yi dubi akan matsayar da suka kai da gwamnati bayan yin yajin aiki a watan Janairu da Fabrairun 2021 tare da nuna rashin jin dadin yadda har yanzu ba a cika musu alkawuran su ba.

JAC ta lissafo tarin dalilan ta na shirin tafiya yajin aiki

Takardar mai take: “Jan kunne dangane da mummunan yanayin da jami’o’i suke ciki” kamar yadda The Sun ta bayyana wacce sakatare janar na NASU, Prince Peters Adeyemi da shugaban kungiyar SSANU, Mohammed Ibrahim, suka sa hannu, JAC ta ja kunne akan cewa ba za ta ci gaba da bayar da tabbacin ayyuka za su ci gaba a jami’o’i ba.

Kara karanta wannan

Majalisar Najeriya za ta sa baki domin Kungiyar ASUU ta janye yajin-aiki, a bude Jami’o’i

JAC ta bayyana bukatun da ta bayar, ciki har da rashin biyan su ta IPPIS, rashin biyan kudaden alawus, daukan lokaci mai tsawo da gwamnatin tarayya ta yi kafin a zauna teburin yarjejeniya da sauran su.

Sauran abubuwa sun hada da rashin biyan kudi ko kuma karanta biyan ma’aikata masu murabus hakkin su wanda hakan ya ci karo da yarjejeniyar su.

Kamar yadda takardar tazo:

“Muna sanar da kowa cewa har yanzu gwamnati bata cika alkawarin da ta dauka ba. Babu wani alkawarin da ta cika daga yarjejeniyar Oktoban 2020 da na Fabrairun 2021 har yanzu.”

Kamar yadda kungiyoyin suka bayyana, shirin IPPIS yana da matsaloli, JAC ta dade da sanar da gwamnati hakan har ta gabatar da shirin biyan ta wanda ta aminta da shi na Universities Peculiar Personnel Payroll System, U3PS.

Gwamnati ta ki zama da kungiyar

Har yanzu gwamnati bata gayyaci JAC don su yi taro ta yi bayani dangane da shirin ba balle har gwamnati ta amince da shi.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Abin da APC ta fada sa’ilin da ASUU ta yi dogon yajin-aiki a mulkin Jonathan

Dangane da alawus, JAC ta ce gwamnati ta yarda da cewa za ta saki naira biliyan 30 don biyan kudin EA inda tace gwamnati ta tozarta yarjejeniyar ta saki kaso 24%, Naira biliyan 22 a watan Disamban 2021.

Kungiyar ta ce gwamnatin tarayya bata sake gayyatar ma’aikatan ba tun 2020 duk da ta amince za ta kammala komai a wata Disamban 2021.

Hakan yasa kungiyar ta yi barazanar tafiya yajin aiki sakamakon matsalolin nan tunda har yanzu gwamnati bata motsa ba kuma bata da niyyar yin komai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel