Majalisar Najeriya za ta sa baki domin Kungiyar ASUU ta janye yajin-aiki, a bude Jami’o’i

Majalisar Najeriya za ta sa baki domin Kungiyar ASUU ta janye yajin-aiki, a bude Jami’o’i

  • Majalisar wakilai ta tabo maganar yajin-aikin da ake yi a jami’o’i a zaman farkon da tayi a makon nan
  • Honarabul Dozie Nwankwo ya koka a game da yadda malaman jami’o’i suke shiga yajin-aiki bini-bini
  • ‘Dan Majalisar na Anambra ya bada shawarar komawa MoU da aka sa wa hannu domin a ceci dalibai

Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta bukaci gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU su yi aiki da yarjejeniyar MoU da aka sa hannu a wajen shawo kan sabaninsu.

Kamar yadda Channels TV ta fitar da rahoto, ‘yan majalisar tarayyan sun nemi gwamnati da malaman jami’an su sasanta domin albarkacin daliban kasar nan.

A zaman da majalisar tayi a ranar Talata, 22 ga watan Fubrairu 2022, an bukaci kwamitocin kwadago da na ilmi a majalisar ya sa baki a kan batun yajin-aikin.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Abin da APC ta fada sa’ilin da ASUU ta yi dogon yajin-aiki a mulkin Jonathan

Kwamitocin za su zauna da ma’aikatun da abin ya shafa da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin kungiyar malaman jami’an sun janye yajin-aikin da suke yi.

Hon. Dozie Nwankwo ya sa baki

Majalisar wakilan kasar ta cin ma wannan matsaya bayan Dozie Nwankwo ya gabatar da kudiri domin ganin an kawo karshen yajin-aikin da ASUU ke yawan yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majalisar Najeriya
Zaman Majalisar Wakilan Tarayya Hoto: HouseNGR
Asali: Facebook

Hon. Dozie Nwankwo ya ce dalibai sun cutu a wancan yajin-aiki na watanni tara da ASUU ta yi.

Punch ta ce ‘dan majalisar na jihar Anambra ya koka a kan yadda rufe jami’o’in yake kawo cikas wajen karatun yara da kai ga tabarbarewar makarantun gwamnati.

Ganin shugaban majalisa da NIREC sun gaza hana yajin-aikin, Nwankwo ya ce mafita ita ce a komawa yarjejeniyar da ASUU da gwamnati suka sa hannu a 2009.

Abin da kunya

Kara karanta wannan

Kun mayar da lakcarori bayi: ASUU ta caccaki gwamnatin Buhari kan batun albashi

A cewar Nwankwo, majalisa ta damu a dalilin yadda ake yawan shiga yajin-aiki a Najeriya, har ta kai abin ya zama abin kunya, kuma yana taba harkar ilmi a kasar.

Majalisa ta karbi korafin da Nwankwo ya kawo, ta bukaci wadannan kwamitoci su zauna da gwamnati, ASUU, NIREC da kuma kungiyoyi domin a samu mafita.

Tuna baya

A jiya mun kawo maku abin da APC ta fada da aka tafi yajin-aiki a 2013. Jam'iyyar ta fito tayi jawabi, tana kiran gwamnati ta cika alkawuran da tayi wa ASUU.

Tsakanin 2011 da 2015, Goodluck Jonathan ne yake mulki, Jam’iyyar APC kuma ta na adawa. A lokacin Lai Mohammed ya nuna goyon bayansu ga malaman jami'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel