Da Dumi-Dumi: Kotu ta umarci a ba tsohon AGF dama ya tafi neman lafiya Amurka

Da Dumi-Dumi: Kotu ta umarci a ba tsohon AGF dama ya tafi neman lafiya Amurka

  • Kotun tarayya dake zama a Abuja ta ba da umarnin sakin Fasfon tsohon Antoni Janar domin ya tafi Amurka a duba lafiyarsa
  • Alkalin Kotun ya umarci Muhammed Adoke, ya tabbata ya dawo da Fasfon cikin kwana uku bayan ya dawo
  • Tsohon Antoni Janar, Muhammad Adoke na fama da shari'a kan abin da ya shafi karkatar da kudaden gwamnati

Abuja - Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta amince da rokon tsohon Antoni Janar na ƙasa, AGF Mohammed Adoke, na neman izinin tafiya kasar amurka a duba lafiyarsa.

Alkalin Kotun, mai shari'a Inyang Ekwo, yayin da yake yanke hukunci ranar Jumu'a, ya ba da umarnin a saki Fasfon tsohon AGF ɗin domin ya samu damar neman Biza.

Haka nan mai shari'a Ekwo, ya umarci Muhammed Adoke ya maida Fasfon cikin kwana uku da zaran ya dawo gida Najeriya, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotu ta yiwa kasurgumin mai garkuwa da mutane, Evans, hukuncin daurin rai da rai

Muhammed Adoke
Da Dumi-Dumi: Kotu ta umarci a ba tsohon AGF dama ya tafi neman lafiya Amurka Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

An gurafanar da tsohon Ministan shari'an a gaban Kotu bisa tuhume-tuhume da suka shafi almundahana da kuɗaɗen gwamnati.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muhammed Adoke na fama da zargin karkatar da kuɗaɗe a gaban Kotun ne tare da babban ɗan kasuwan nan, Aliyu Abubakar.

Tuni aka girke Fasfon Adoke a gaban Alkali a wani ɓangare na cika sharuɗɗan Belin da Kotun ta ba shi tun farko, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

Yaushe ya nemi izinin zuwa Amurka?

Adoke, a cikin takaradar rokon da ya shigar mai ɗauke da kwanan watan 24 ga watan Fabarairu, ya ce yana bukatar Fasfon ne saboda, "ya samu damar neman Bizar lafiya ya shiga ƙasar Amurka."

Ya kara da bayanin cewa, "Hakan zai sa na halarci ranar da aka bani a Asibitin Cleveland Hospital, dake Ohio, a kasar Amurka, domin duba ciwan dake damu na."

Kara karanta wannan

Alkali ya bada umarni hukumar EFCC ta karbe gidan tsohon Gwamnan APC a Abuja

A wani labarin kuma Kotu ta bada umarnin kwace kadarori 10, da kudaden Banki na tsohon gwamnan Zamfara

Kotun tarayya a Abuja ta ba da izinin kwace kadarori kusan 10 da makudan kudin dake kwance a Banki mallakin Abdul'aziz Yari.

Alkalin Kotun ya ce umarnin na wucin gadi zai kwashe kwanaki 60, kuma bayan haka ICPC zata iya neman kwace su har abada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel