Da duminsa: Kotu ta yiwa kasurgumin mai garkuwa da mutane, Evans, hukuncin daurin rai da rai

Da duminsa: Kotu ta yiwa kasurgumin mai garkuwa da mutane, Evans, hukuncin daurin rai da rai

  • Bayan shekaru hudu ana kai ruwa rana a kotu, an yanke hukuncin daurin rai da rai kan Evans
  • Kasurgumin mai garkuwa da mutanen na cikin manyan barayin da dakataccen dan sanda Abba Kyari ya kama
  • Alkalin da ya yanke hukunci ya bayyana cewa Evans ko nadamar abubuwan da yayi ba ya yi

Wata kotun jihar Legas dake zamanta a Ikeja ta yankewa kasurgumin mai garkuwa da mutane, Chukwudimeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans hukuncin daurin rai da rai.

An yankewa Evans da abokan huldansa biyu, Uche Amadi, da Okwuchukwu Nwachukwu, ne bayan kamasu da laifin garkuwa da mutane.

Alkali Hakeem Oshodi wanda ya yanke hukunci ya ce an kama su ukun da laifi ne bayan hujjoji sun nuna cewa lallai sun aikata laifukan da ake zarginsu da shi.

Kara karanta wannan

Evans: Ko Kaɗan Bai Nuna Alamar Nadama Ba Yayin Shari’arsa Na Shekaru Hudu, Alƙali

Da duminsa: Kotu ta yiwa kasurgumin mai garkuwa da mutane, Evans, hukuncin daurin rai da rai
Da duminsa: Kotu ta yiwa kasurgumin mai garkuwa da mutane, Evans, hukuncin daurin rai da rai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alkalin ya kama su dumu-dumu da aikata laifukan

Alkalin ya yanke musu hukunci bayan kama su sa laifukan makirci da kuma garkuwa da mutane.

Sai dai ya wanke Ogeshi Uchechukwu, Chilaka Ifeanyi wanda tsohon soja ne tare da sallamar wani Victor Aduba, wanda shima tsohon soja ne.

Tun asali Evan ya ce azabar da ‘yan sanda suka yi masa ne ya sanya ya dinga murmushi yayin amsa laifinsa

Da farko Oshodi ya yi fatali da korafin da Evans ya yi akan illar da ‘yan sanda suka yi masa kamar yadda ya bayyana, wanda hakan ya ci karo da sashi na 9(3) na Administration Criminal Justice.

Alkalin ya ce bidiyoyi biyu na Evans wanda aka nuna wa kotu sun bayyana shi yana murmushi yayin da yake bayyana laifukansa.

Ya kara da cewa idan mutum ya yi dubi da bidiyon zai gane cewa babu wata alamar azaba a jikin sa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya zata kwaso yan Najeriya dake zaune a kasar Ukraniya

Oshodi ya nuna inda Evans ya yi ikirarin cewa yana gida tare da matarsa a ranar 14 ga watan Fabrairu da aka yi garkuwa da Dunu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel