Wani Matashi ya shakare mahaifiyarsa har Allah ya mata rasuwa a Gombe

Wani Matashi ya shakare mahaifiyarsa har Allah ya mata rasuwa a Gombe

  • Hukumar yan sanda ta jihar Gombe ta damke wasu mutum 8 da aikata laifuka kala daban-daban a faɗin jihar
  • Daya daga cikinsu, Garba Abubakar, ana zargin ya shake mahaifiyarsa har Lahira saboda ta masa fada ya daina mugayen hali
  • Wani kuma ya yi lalata da ɗiyar makocinsa, wacce ke kai masa tallan abincin dabbobi yar shekara 10 kacal a duniya

Gombe - A jiya Laraba, hukumar yan sanda reshen jihar Gombe ta jera wasu mutum takwas da ta kama da laifi daban-daban a faɗin jihar.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa ɗaya daga cikinsu, Garba Abubakar, ya shiga hannu ne bisa zargin shakare mahaifiyarsa, Salamatu Abubakar, yar shekara 45.

Hukumar yan sanda
Wani Matashi ya shakare mahaifiyarsa har Allah ya mata rasuwa a Gombe Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kwamishinan yan sandan jihar Gombe, Ishola Babaita, ya ce wanda ake zargin ya yi wa mahaifiyarsa haka ne saboda ta masa faɗa ya daina shan miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An bindige shugaban al'umma dake jiran gadon Sarauta a cikin gida, Allah ya masa rasuwa

Kwamishina ya ce:

"Wanda ake zargi ya shake mahaifiyarsa ne saboda ta masa faɗa ya dena ta'amali da miyagun kwayoyi. An yi gaggawar kai matar babban Asibitin Kumo, amma likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa."
"Ina shawartar iyaye su maida hankali da sa ido wajen kula da 'ya'yan su kuma su tabbatar ba su faɗa muguwar ɗabi'ar shan miyagun kwayoyi ba."
"Babban abun takaici wannan matar ta rasa rayuwarta a hannun ɗan da ta tsugunna ta haifa, ɗaya ne daga cikin sharrin kwayoyi."

Wani ya yi lalata da ɗiyar makocinsa

Wani na daban kuma daga cikin waɗan da ake zargin, Adamu Lawal, ɗan shekara 53, ya hayayyaƙe wa diyar makocinsa yar shekara 10 ta dole.

Yarinyar ta kasance ta na kai masa abincin dabbobi yana siya, amma sai ya yi amfani da wannan damar wajen ɓata mata rayuwa.

Kara karanta wannan

Rikita-Rikita: Wani mutumi da aka ce ya mutu ya dawo gida bayan shekara 5, Matarsa ta guje shi

"Wannan mutumin ya yi amfani da zuwan yarinyar, ya haye mata ta tsiya, yarinya karama da ba ta mallaki hankalinta ba."

Jirgi ya yi saukar gaggawa a Abuja

A wani labarin kuma kun ji yadda matukin wani jirgin Dana Air ya yi gaggawar sauke jirgin sabida wasu dalilai da ka iya jawo hatsari

Jirgin wanda ya taso da nufin kai Fasinjojinsa jihar Legas, ya dira a babban birnin tarayya Abuja da tsakar rana misalin karfe biyu da wasu mintuna

Bayan wani lokaci kamfanin jirgin ya samar da wani Jirgi na daban domin cika wa fasinjojinsa bukatarsu ta zuwa Legas, ya ba su hakurin tsaikon da aka samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel