Sabon yaki ya barke tsakanin Rasha da Ukraniya, Rasha ta fara kai harin bama-bamai

Sabon yaki ya barke tsakanin Rasha da Ukraniya, Rasha ta fara kai harin bama-bamai

  • Ministan harkokin wajen Ukraniya ya yi kira ga kasashen duniya su kawo mata dauki yayinda Rasha ta fara kai musu hari
  • Shugaban kasar Rasha , Vladimir Putin, ya bayyanawa al'ummar kasarsa cewa zasu fara kai hari Ukraniya
  • Wannan rikicin ya biyo bayan yunkurin da Ukraniya ke yi na shiga kungiyar mayaka ta NATO

Dakarun Sojin kasar Rasha sun harba makami mai linzami cikin biranen Ukraniya yayinda Sojin kasa suke kokarin shiga, jami'an gwamnati da manema labarai sun bayyana.

Wannan ya biyo bayan sanarwar da Shugaban kasar Rasha, Vlamidir Putin, yayi cewa zasu fara kai hari gabashin Ukraniya.

Yan mintuna bayan sanarwar Putin a tashar Talabijin na kasar aka fara jin karar bama-bamai cikin birnin tarayyar Ukraniya, Kyiv.

Ministan harkokin wajen Ukraniya, Dmytro Kuleba, a jawabin da ya saki a shafinsa na Tuwita yace:

Kara karanta wannan

Shugaban 'yan bindiga, Dullu Kachalla, ya sassauta kudin haraji ga mazauna saboda sun gagara biya

"Putin ya fara kai hari Ukraniya. Ana kaiwa biranen Ukraniya hari."
"Wannan yaki ne da zalunci. Ukraniya zata kare kanta kuma zamuyi nasara. Wajibi ne duniya ta dakatad da Putin kuma zata iya. Lokaci yayi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin Shugaban kasar Amurka

Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya yi barazanar kakabawa Rasha takunkumi kan hare-haren da take kaiwa Ukraniya.

Martani kan harin da Rasha ta fara kaiwa, yace:

"Zan gana da Shugabannin G&, kuma Amurka da kawayenta zasu kakawa Rasha takunkumi mai karfi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel