Zaria: Kotu Ta Umurci a Kamo Matar Aure Da Ake Zargin Ta Keta Fuskokin Yaran Kishiyarta Da Reza

Zaria: Kotu Ta Umurci a Kamo Matar Aure Da Ake Zargin Ta Keta Fuskokin Yaran Kishiyarta Da Reza

  • Wata kotun majistare da ke Sabon Garin Zaria a ranar Alhamis ta bukaci ‘yan sanda su kamo wata matar aure, Basira Auwal, bisa zargin ta da ji wa yaran kishiyar ta munanan raunuka
  • Alkalin kotun, Toro Luka ya bayar da umarnin kamo matar ne bayan ta ki gabatar da kan ta gaban kotu kamar yadda mai gabatar da kara, Sifeta Napko Renbuk ya shaida wa kotun
  • Ana zargin matar da lallabawa dakin yaran kishiyar ta inda ta samu reza ta dinga tsaga fuskokin yaran guda biyu har sai da ta yi kaca-kaca da su, daga nan aka zarce da su asibiti cikin gaggawa

Jihar Kaduna - A ranar Alhamis, wata kotun majistare da ke Sabon Garin Zaria ta bukaci a kamo wata Basira Auwal bisa zargin ta da ji wa yaran kishiyar ta miyagun raunuka, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu: Mai aski zai yi sharar caji ofis na kwana 90 saboda samunsa da laifin damfarar kudi ta intanet

Alkalin kotun, Toro Luka ya bayar da umarnin damko ta ne bayan mai gabatar da kara, Sifeta Napko Renbuk ya sanar da kotu cewa ya kamata a fara sauraron karar amma ba zai yiwu ba saboda wacce ake kara ba ta bayyana a kotun ba.

Cin Zalin Yaran Kishiya: Kotu Ta Umurci a Kamo Wata Matar Aure a Zaria
Kotu Ta Umurci a Kamo Wata Matar Aure a Zaria Kan Zargin Cin Zalin Yaran Kishiyarta. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Don haka mai gabatar da kara ya bukaci a kamo ta kamar yadda sashi na 127 na Criminal Justice Act 2017 ya tanadar. Alkali Luka ya amince da bukatar kamo ta.

Alkalin ya janye belin wacce ake kara kuma ya dage sauraron shari’ar

Alkalin ya janye belin wacce ake karar bayan ya amince a baya kamar yadda Vanguard ta nuna. Sannan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Fabrairu don sauraron shari’ar.

Kara karanta wannan

Kaduna: Kotun Shari'a Ta Tura Kishiyoyi 2 Zuwa Gidan Yari Saboda Faɗa Kan Mijinsu, Mijin Ya Ce Akwai Yiwuwar Ya Sake Su Duka

Kamar yadda rahoton ‘yan sanda ya bayyana, a ranar 7 ga watan Fabrairu, Shamsiyya Mohammed ta kauyen Bomo, Sabon-Gari Zaria ta gabatar da korafi akan wacce ake karar zuwa ofishin ‘yan sanda da ke Samaru.

‘Yan sanda sun shaida yadda lamarin ya auku ranar 8 ga watan Janairu bayan wata hayaniya ta shiga tsakanin Mohammed da wacce ake karar.

Wacce ake kara ta shiga dakin yaran ne inda ta yayyanka fuskokin su da reza

Mohammed ta ci gaba da bayyana yadda wacce ake karar ta lallaba dakin yaranta ta yi amfani da reza wurin yayyanka fuskokin yaran guda biyu, daya mai shekaru 12 dayan kuma shekarun sa 9.

‘Yan sanda sun sanar da yadda aka zarce da yaran asibitin koyarwa na Ahmadu Bello inda ake kulawa da lafiyarsu yanzu haka.

A ranar 9 ga watan Fabrairu aka gurfanar da Auwal gaban kotu.

Laifin ya ci karo da sashi na 223, 228 da 240 na dokar Penal Code ta Jihar Kaduna da kuma sashi na 2 na cutar da bil’adama, dokar 2015.

Kara karanta wannan

2023: Wata Ƙungiya Ta Sake Shawartar Atiku Ya Haƙura Da Batun Sake Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa

Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki

A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.

Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.

Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.

Asali: Legit.ng

Online view pixel