Kotu ta sake umartar 'yan sanda su kamo Jaruma mai sayar da kayan-mata

Kotu ta sake umartar 'yan sanda su kamo Jaruma mai sayar da kayan-mata

  • Babbar kotun da ke zama a Zuba cikin babban birnin tarayya, Abuja ta kara bayar da umarnin kamo fitacciyar mai sayar da kayan-mata, Hauwa Muhammed wacce aka fi sani da Jaruma
  • Jaruma ta gurfana gaban kotu a ranar 25 ga watan Janairu bisa zarginta da yin batanci, kago labaran karya da cin zarafin gawurtaccen dan kasuwa, Ned Nwoko a kafafen sada zumunta
  • Nwoko ya zargi Jaruma da wallafe-wallafen karya a shafinta na Instagram akan shi da matarsa, Regina Daniels wanda har alkali ya sa aka rufe ta a gidan gyaran hali da ke Suleja daga bisani ya bayar da belin ta

Abuja - Babbar kotun da ke zama a Zuba, cikin babban birnin tarayya ta bayar da umarnin a damko sananniyar mai sayar da kayan-mata, Hauwa Muhammed wacce aka fi sani da Jaruma, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

An gurfanar da ita gaban kotu a ranar 25 ga watan Janairu bayan an zarge ta da bata suna da wallafar karairayi a kafafen sada zumunta akan babban dan kasuwa, Ned Nwoko.

Kotu ta kara umartar 'yan sanda su kamo Jaruma mai sayar da kayan-mata
Kotu ta kara umurci 'yan sanda su kamo Jaruma mai sayar da kayan-mata. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Nwoko ya zargi Jaruma da yin wallafe-wallafe na labaran karya a shafinta akan matarsa, Regina Daniels da shi kan shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tun farko alkali ya ja kunnen bangarorin guda biyu akan ci gaba da maganganu

Alkali, Ismailia Abdullahi ya yanke hukunci akan a rufe Jaruma a gidan gyaran halin Suleja kafin a amince da belin ta kamar yadda The Punch ta bayyana.

Sannan ya ja kunnen duk bangarorin akan daina yin maganganu ko wasu wallafe-wallafe saboda kotu zata yi alkalanci akan duk abinda suka yi.

An saki Jaruma a ranar 28 ga watan Janairu bayan ta cika sharuddan beli.

Kara karanta wannan

NDLEA ta cafke kudi har $4.7 na jabu a Abuja, ta yi ram da maijego dauke da kwayoyi

Yayin da za a ci gaba da sauraron karar a ranar Laraba, Jaruma bata bayyana a kotu ba.

Alkalin ya zarge ta da kin bayyana a kotu duk da ta san ranar za a ci gaba da shari’ar kuma hakan cin mutuncin shari’a.

Alkali ya bayar da umarnin kamo Jaruma da tsayayyen ta don su yi wa kotu bayani akan rashin zuwanta

A cewarsa:

“Wacce ake kara ta san cewa yau ne ake ci gaba da shari’ar amma ta ki zuwa kotun.
“Idan ba a dauki hukunci ba kamar cin mutuncin shari’a ta yi, kamar yadda sashi na 131 ya tanadar a dokar Criminal Justice kuma bayan sauraron korafin bangaren da suka kai karar. Don haka na bayar da umarnin kamo Hauwa Mohammed wacce aka fi sani da Jaruma sannan mun bayar da umarnin kamo tsayayyen ta don ya zo kotu ya shaida dalilin da ya hanata zuwa kotun.”

An dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Maris din 2022.

Kara karanta wannan

Kotun shari'a ta sa an jefe mace da namiji bayan an kama su dumu-dumu suna lalata

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

A wani labarin daban, a ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.

Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel