Hannun jari: Yadda kamfanin sukarin Dangote ya rage daraja da kusan N11bn saboda rikici da BUA

Hannun jari: Yadda kamfanin sukarin Dangote ya rage daraja da kusan N11bn saboda rikici da BUA

  • Rikici tsakanin kamfanin sukarin Dangote da kayan abinci na BUA ya koma kan kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya inda sukarin Dangote ya sauka kasa
  • Yayin harkalla ciniki ta ranar Laraba, 23 ga Fabrairu, 2022, farashin hannun jarin kamfanin sukarin Dangote ya ragu da 5.28% bisa dari
  • Darajar harkallar kamfanin ya ragu daga Naira biliyan 218 zuwa Naira 207.10 inda kasuwa ta rufe kan Naira 17.05 kan kowane hannu

Rikici tsakanin kamfanin BUA da na sukarin Dangote ya zama mai girma a masana'antar sukari, kuma alamu na nuna tafiyar ta fi karbar BUA wanda ya zargi kamfanin sukarin Dangote kwanan nan da son haifar da karancin sukari.

A cinikayyar ranar Laraba, 23 ga Fabrairu, 2022, farashin hannun jarin kamfanin sukarin Dangote ya ragu da 5.28%, inda kasuwa ta rufe yana da Naira 17.05 kan kowane hannu, farashin kasuwarsa ya sauka kenan daga Naira biliyan 218 zuwa Naira biliyan 207.10.

Kara karanta wannan

Harkallar kwaya: Kotu a Abuja ta ce NDLEA ta duba bukatar belin Abba Kyari cikin awa 48

Kamfanin sukarin Dangote ya tafka asara
Hannun jari: Yadda kamfanin sukarin Dangote ya rage daraja da kusan N11bn saboda rikici da BUA | Hoto: businessday.ng

Yadda kamfanin sukarin Dangote ya sauka a kasuwar hannun jari

Kamfanin sukarin ya sami raguwar farashin hannun jari, kuma za a iya danganta shi da sauyin ra'ayin masu zuba hannun jari wanda ya haifar da sayar da hannayen jari a kamfanin kan kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hannayen jarin FMCG sun ragu daga N18.00 a farkon hada-hadar kasuwancin kuma ya rufe a kan N17.05 a kowane hannu, wanda ke nuna raguwar 5.28%, kamar yadda Legit.ng ta tattaro.

Takaitaccen bayani kan hada-hada a kasuwar hannun jari

Kamfanin mai samar da sukari ya samu bahagon tasiri a kan darajar kasuwarsa da ta sauka daga Naira biliyan 218.64 zuwa Naira biliyan 207.10 a karshen hada-hadar kasuwancin ranar Laraba.

Hannun jarin kamfanin sukarin Dangote ya ragu da kashi 2.01% daga farkon shekarar nan zuwa yanzu, inda ya fara hada-hadarsa a kan N17.40 kuma a halin yanzu yana kan hada-hada da N17.05, wanda ke nuna raguwa.

Kara karanta wannan

A Cikin Awa 24 Kacal, Ɗangote Ya Samu Kuɗin Da Ya Ɗara Na Elon Musk Da Bill Gates

Hannun jarin kamfanin a halin yanzu ya kai 9.07% kasa da mako 52 wanda ya kai N18.75 a kan kowanne hannu.

Sai dai kuma hannun jarin kamfanin ya dawo da kusan ribar 13.67% ga masu zuba jarin da suka saya a kan farashi mai rahusa a mako 52 (N15.00 kan kowane hannu) daga ranar hada-hadar da ta gabata, inda kasuwa ta rufe a kan maki 47,207.27 da kuma habakar Naira tiriliyan 25.44.

A cikin awa 24 kacal, Dangote ya samu kudin da ya dara na Elon Musk da Bill Gates

A wani labarin kuma, kudin Attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya samu karuwa da Naira biliyan 28.86 (69.4 million) cikin awa 24.

A cewar Bloomberg, arzikin Dangote a yanzu ya kai Dallar Amurka biliyan 20, hakan ya sa ya zama mutum na 83 cikin jerin attajiran da suka fi kowa kudi a duniya bayan farfadowarsa daga makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Rashin wutan lantarki ya zama tarihi a Najeriya, Ministan Buhari

Tunda ya kafa kamfaninsa a shekarar 2022, arzikin Dangote ya karu da $934 million (N388.5bn) saboda cigaban da ake samu a kamfaninsa na siminti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel