A Cikin Awa 24 Kacal, Ɗangote Ya Samu Kuɗin Da Ya Ɗara Na Elon Musk Da Bill Gates

A Cikin Awa 24 Kacal, Ɗangote Ya Samu Kuɗin Da Ya Ɗara Na Elon Musk Da Bill Gates

  • Wannan sabbin kudaden da Dangote ya samu ya saka shi ya samu cigaba daga matsayinsa na 91 zuwa na 83 cikin jerin attajitan duniyaya
  • Wannan sabbin kudaden da Dangote ya samu ya sak shi ya samu cigaba daga matsayinsa na 91 zuwa na 83 cikin jerin attajiran duniya
  • Mafi yawancin arzikin Aliko Dangote yana da alaka ne da kamfaninsa, Dangote Cement Plc, hakan yasa duk lokacin da kudin hannun jarin ya canja sai arzikinsa ya canja

Kudin Attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya samu karuwa da Naira biliyan 28.86 (69.4 million) cikin awa 24.

A cewar Bloomberg, arzikin Dangote a yanzu ya kai Dallar Amurka biliyan 20, hakan ya sa ya zama mutum na 83 cikin jerin attajiran da suka fi kowa kudi a duniya bayan farfadowarsa daga makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Ina tare da dalibai mata Musulmai, babu wanda ya isa ya hanasu sanya Hijabi: Gwamnan Kwara

A Cikin Awa 24 Kacal, Ɗangote Ya Samu Kuɗin Da Ya Ɗara Na Elon Musk Da Bill Gates
A Cikin Awa 24, Ɗangote Ya Samu Kuɗin Da Ya Ɗara Na Elon Musk Da Bill Gates. Hoto: Bloomberg
Asali: Facebook

Tunda ya kafa kamfaninsa a shekarar 2022, arzikin Dangote ya karu da $934 million (N388.5bn) saboda cigaban da ake samu a kamfaninsa na siminti.

Attajiran duniya sun tafka manyan asara

A yayin da arzikin Dangote ya karu, mutane biyar mafi arziki a duniya, Elon Musk, Jeff Bezos, Bernard Arnault da Bill Gates su kuma kudinsu raguwa ya yi.

Alkalluman Bloomberg sun nuna cewa a cikin awa 24, Elon Musk ya tafka asara ta Dalar Amurka biliyan 8.4 yayin da Jeff Bezos ya rasa Dalar Amurka 2.43 biliyan.

Mutane na uku da hudu cikin jerin attajiran duniya Bernard Arnault da Bill Gates su ma arzikinsu ya ragu da Dala Biliyan 3.13 da Dala 886 miliyan.

Mai kamfanin Facebook (Meta) shima ya tafka babban rashi a ranar inda ya rasa Dala biliyan 1.8 cikin arzikinsa.

Kara karanta wannan

Muna shirin karban sabon bashin $3bn don kammala wasu ayyuka 10, Ministar Kudi

Wannan sabon arzikin na Dangote ya saka ya sake bai wa mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Roman Abramovich, tazara, wanda ke mataki na 124 da kudi $15.4

Asali: Legit.ng

Online view pixel