Da dumi: Mutum 2 sun hallaka, an yiwa wasu jina-jina a zaben deleget na PDP

Da dumi: Mutum 2 sun hallaka, an yiwa wasu jina-jina a zaben deleget na PDP

  • Jam'iyyar PDP a jihar Osun na gudanar da zaben deleget da zasu yi zabi wanda za'a baiwa tutar jam'iyyar a zaben gwamna
  • Wannan zabe ya rikide ya koma rikici inda aka fara rashin rayuka kuma wasu sun jigata
  • Kawo yanzu Alkalin zaben, Gwamnan jihar Adamawa, Ahmad Fintiri, basu isa wajen tattara zabe ba

Osogbo - Akalla mutum biyu sun rasa rayukansu yayinda da dama suka jikkata a zaben deleget na jam'iyyar People’s Democratic Party PDP dake gudana a jihar Osun.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Yemisi Opalola, ta tabbatar da hakan ga manema labarai ranar Laraba a Osogbo, TVCNews ta ruwaito.

A cewarta, an kashe wani matashi mai suna Toheeb Mutallib a Oke Oba, Agberire a karamar hukumar Iwo, yayinda aka kashe wani dan jam'iyyar siyasa Aremu Olamide a Ipetumodu, karamar hukumar Ife-North.

Kara karanta wannan

Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

Rikici
Da dumi: Mutum 2 sun hallaka, an yiwa wasu jina-jina a zaben deleget na PDP Hoto: @tvcNews
Asali: Twitter

Wasu masu idanuwan shaida sun bayyana cewa an yiwa mutane da dama jina-jina yayinda yan daba suka kai hari garuruwa irinsu Ede, Osogbo, Odo-Otin, Olorunda, Iwo, da sauransu.

Hakazalika an bankawa mota wuta a Ipetumodu sakamakon rikici tsakanin yan daba.

Kawo yanzu Alkalin zaben, Gwamnan jihar Adamawa, Ahmad Fintiri, basu isa wajen tattara zabe ba.

Za'a zabi mutum uku-uku a gundumomin jihar 332 kuma su zasu kada kuri'a a zaben fidda gwanin dan takaran gwamna a ranar 7 ga Maris, 2022.

Da dumi: Mutum 2 sun hallaka, an yiwa wasu jina-jina a zaben deleget na PDP
Da dumi: Mutum 2 sun hallaka, an yiwa wasu jina-jina a zaben deleget na PDP
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel