Tsohuwar Minista Da Kotu Ta Yi Wa Ɗaurin Shekara 3 Ta Magantu, Ta Bayyana Matakin Da Ta Ɗauka

Tsohuwar Minista Da Kotu Ta Yi Wa Ɗaurin Shekara 3 Ta Magantu, Ta Bayyana Matakin Da Ta Ɗauka

  • Mrs Sarah Ochekpe, Tsohuwar Ministan Albarkatun Ruwa ta kotu ta yanke wa hukuncin daurin shekaru 3 kan zargin karbar N450m ta ce bata gamsu da hukuncin ba
  • Ochekpe da sauran mutanen biyu da aka yanke wa hukuncin sun ce sun umurci lauyoyinsu suyi nazarin hukuncin su sanar da su matakin da za su dauka
  • Kotun ta saki Mrs Ochekpe ne da shugaban wucin gadi na PDP, Jihar Plateau, Hon Raymond Dabo da Leo Jitung bayan sun biya N1m

Tsohuwar Ministan Albarkatun Ruwa, Mrs Sarah Ochekpe ta ce bata gamsu ba da hukuncin babban kotun tarayya da ta yanke mata daurin shekaru uku da wasu mutane biyu kan zargin cire kudi Naira miliyan 450, wanda hakan ya saba ka'ida.

An yanke mata hukuncin tare da shugaban wucin gadi na PDP, Jihar Plateau, Hon Raymond Dabo da Leo Jitung kamar yadda The Sun ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

Tsohuwar Minista Da Kotu Ta Yi Wa Ɗaurin Shekara 3 Ta Magantu, Ta Bayyana Matakin Da Ta Ɗauka
Tsohuwar Ministan Ruwa Da Kotu Ta Yi Wa Ɗaurin Shekara 3 Ta Magantu, Ta Bayyana Matakin Da Ta Ɗauka. Hoto: The Sun
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce hukuncin da aka yi wanke su bisa zargin bannatar da kudi tunda an gano cewa sun mika kudin ga kwamitin yakin neman zabe na jihar.

Mai shari'a Musa Kurna na Babban Kotun Tarayya a Jos, wanda ya yanke hukuncin ya kuma ba su zabin biyan tara ta Naira miliyan 1.

Mrs Ochekpe, wacce ta yi martani kan hukuncin a St Jarlath Secondary School Bukuru, inda ta ke koyarwa ta ce ta bukaci lauyoyinta su yi nazarin hukuncin domin su bata shawarar matakin da za ta dauka, rahoton The Sun.

Ta bayyana cewa kowannensu ya biya Naira miliyan daya kuma an kyalle su su tafi gida.

Mrs Ochekpe ta yi bayanin abin da ya faru

Ochekpe ta ce EFCC ta gayyaci su zuwa ofishinta a Gombe a 2016, suka amsa gayyatar a Janairun 2017.

Kara karanta wannan

Wawure kudin kasa: Kotu ta tasa keyar tsohuwar minista da wasu mutane 2 zuwa gidan yari

Ta ce dukkansu ba su san dalilin da yasa aka gayyace su ba amma jami'an EFCC sun fada musu ana zarginsu ne da rike kudin sata da ya kai Naira miliyan N450m.

"Mun rubuta takarda inda muka ce an yi zaben shugaban kasa da yan majalisar tarayya kuma an turo kudin ne daga Abuja zuwa Jihar Plateau.
"An zabi mutum uku su karbi kudin a madadin PDP na Jihar Plateau, kuma muka karba kudin ba tare da sanin akwai wata matsala ba.
"An bukaci mu bada bayanin kudaden da suka shiga asusun mu na baki sai suka yi ikirarin cewa kudin sata ne muka ce musu ba mu da masaniya kan hakan."

Ta cigaba da cewa an dauko kudin daga banki kuma aka kai ofishin kamfen sannan mai ajiyan kudi ya tabbatar da hakan. Shugaban ALGON shima ya tabbatar an raba kudin domin zaben kananan hukumomi.

"Hakan yasa alkali ya wanke mu daga zargin. Amma aka fada mana cewa an same mu da laifin hadin baki kuma wai ba mu karba kudin ta hukumar da aka amince da rika hada-hadar kudi ba.
"An ci kowannen mu tarar N1m, muka biya sannan muka tafi gida. Mu dai ba mu gamsu da wannan hukuncin kuma mun fada wa lauyoyin mu kuma suna duba abin sannan su bamu shawarar abin da za mu yi," in ji ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel