Gwamnan APC ya rabawa mutum 30000 marasa karfi garin kwaki domin 'inganta tattali'

Gwamnan APC ya rabawa mutum 30000 marasa karfi garin kwaki domin 'inganta tattali'

  • A makon nan aka ji yadda Gwamnatin jihar Osun ta raba gari a wani shiri na‘Food Support Scheme’
  • An kawo wannan tsari domin rage radadin annobar COVID-19 da kuma zaburar da tattalin arziki
  • Ana sa ran hakan zai karfafawa matasa wajen rungumar noma ta yadda mutane zasu samu abin yi

Osun - Jaridar PM News ta kawo rahoto cewa a ranar Litinin, 21 ga watan Fubrairu 2022, Gwamnatin jihar Osun ta raba gari ga masu karamin karfi.

Mai girma Gwamna Gboyega Oyetola ya raba kilo biyar na garin rogo ga mutane 30, 000 a Osun.

Jaridar Sun ta ce wannan rabon kayan abincin da aka yi, yana cikin tsarin ‘Food Support Scheme’ da aka shigo da shi domin rage radadin annobar COVID-19.

Gboyega Oyetola ya raba ledojin garin rogon a sakatariyar gwamnati da ke Abare, garin Osogbo. Prince Wole Oyebamiji ya wakilci gwamna a wajen rabon.

Kara karanta wannan

Dalilin jinkirta taron gangamin APC: Tsohon gwamna ya ce Buni ne ya jawo, yana son ya gaji Buhari a 2023

Sakataren gwamnatin na jihar Osun, Prince Oyebamiji ya bayyana cewa rabon garin zai taimaka wajen habaka tattalin arziki kamar yadda bincike ya nuna.

Gari a leda
Prince Wole Oyebamiji ya na raba gari Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Prince Wole Oyebamiji ya wakilci Gwamna

“Gwamnatinmu ta mutane ce, domin mutane kuma mutane suka cika ta, don haka gwama yake da matukar sha’awar ganin an bunkasa tattalin arzikin jiha.”
“Idan mu na karfafawa samari da ‘yan mata su rungumi noma, mu a matsayinmu na gwamnati, to ya kamata mu rika yi masu ciniki, mu mara masu baya.”
“Harkar noma akwai wahala, ba abu ba ne mai sauki ka yi nasarar ba matasa shawara su koma gona ba tare da ka ba su duk goyon bayan da suke bukata ba.”
“Samar da garin rogo da mutanenmu suke yi ya nuna babu shakka, akwai kudi a noma.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yadda jami'in dan sanda ya mutu a cikin gidan wani tsohon gwamna

- Prince Wole Oyebamiji

Babu nadama a kan wannan aiki

Prince Wole Oyebamiji ya ce ba su yi da-na-sani ba domin matakin da suka dauka zai bunkasa noma, ya inganta tattalin arziki, kuma mutane su samu abin yi.

A madadin gwamna Oyetola, sakataren gwamnatin ya ce bai kamata a raina duk abin da aka raba ba.

Rikicin APC a Osun

Kun ji labarin cewa Gwamna Gboyega Oyetola ne ya sake samun tikitin jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Osun da za ayi. Oyetola ya doke 'yan takara biyu.

Kafin a shirya zaben, Rauf Aregbesola ya yi alkawarin Gwamnan ba zai koma mulki ba. Zaben fitar da gwanin ya sake nuna karfin Bola Tinubu a siyasar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel