Tinubu ya nunawa Ministan Buhari iyakarsa a rikicin jam'iyyar APC kan takarar Gwamna

Tinubu ya nunawa Ministan Buhari iyakarsa a rikicin jam'iyyar APC kan takarar Gwamna

  • Gboyega Oyetola ne ya sake samun tikitin jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Osun da za ayi
  • Kafin a shirya zaben, Rauf Aregbesola ya yi alkawarin Gwamnan ba zai koma karagar mulki ba
  • Oyetola wanda ya ke tare da Bola Tinubu ya yi wa ‘dan takarar Ministan, Adeoti kaca-kaca a zaben

Osun - An kammala zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC mai mulki a jihar Osun, Moshood Adeoti ya sha kashi a hannun Gwamna mai-ci Gboyega Oyetola.

This Day ta ce kafin zaben an yi ta rade-radin APC za ta samu kan ta cikin matsala a sakamakon bullowar wasu ‘yan taware a jihar Osun da suka kira kansu da Top.

Tsohon gwamna Rauf Aregbesola ne ya tsayawa Alhaji Moshood Adeoti. Shi kuma Gboyega Oyetola yana tare da jagoran APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Jagororin Kwankwasiyya sun juyawa Kwankwaso baya, ana kishin-kishin za su tsallaka APC

Shugaban kwamitin APC na zaben fitar da gwani, Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya ce a cikin mutane 247,207, an samu 235,550 da suka kada kuri’a.

Gwamna Abdulrazaq ya ce Gboyega Oyetola ya samu kur’u 222,169, Moshood Adeoti ya samu 12921, sai kuma Yusuf Lasun ne ya zo na karshe da kur’u 460 rak.

Tinubu
Bola Tinubu, Gboyega Oyetola da Rauf Aregbesola Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Rauf Aregbesola ya sha kashi

Oyetola ya tika babban abokin hamayyarsa, Moshood Adeoti da kasa har a mazabar ubangidansa, Rauf Aregbesola na Ilofin a karamar hukumar Ilesa ta gabas.

Rahoton ya ce gwamna Oyetola ya samu nasara a mazabar da kuri’u 309, Adeoti ya samu 146. Hakan ya nuna an yi wa mutanen su Aregbesola ta-tas a zaben.

Aregbesola ya yi kusufi

Duk da cewa Aregbesola ya na jihar Osun a ranar ja-ji-birin zaben, ba a ga duriyarsa a wajen kada kuri’a ba. Majiya ta ce wani aiki ne ya sa ya koma garin Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan siyasa 4 da su ka rike Minista a mulkin Jonathan, yanzu su ne Gwamnonin jihohinsu

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya yi kokarin hana Oyetola tikitin APC, kamar yadda jam’iyyar ta yi wa Akinwumi Ambode a jihar Legas a 2015.

Tsohon gwamnan wanda yake rigima da Tinubu ya sha alwashin zai nemawa bangarensa hakki a kotu, ya ce zai yi kokarin ganin Alkali ya soke nasarar Oyetola.

Adeoti wanda ya yi sakataren gwamnati a Osun ya ce ba ayi masa adalci ba, ya zargi shugabannin APC na kasa da goyon bayan Oyetola, wanda ya ce ya tafka magudi.

Buratai a 2023?

Dazu aka ji Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) ya ba masoya da ke zuga shi ya fito neman takarar shugaban kasa kunya, ya ce bai da niyyar shiga siyasa.

Sani Usman Kukasheka ya fitar da jawabi a madadin Janar Buratai ya nuna bai san da zaman masu kiraye-kiraye da fito da fastocin neman takararsa a 2023 ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya yi magana a kan takarar Tinubu da Osinbajo a zaben Shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel