Babban bako a villa: Buhari ya karbi bakuncin takwaransa na kasar Ghana

Babban bako a villa: Buhari ya karbi bakuncin takwaransa na kasar Ghana

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin takwaransa na Ghana, Nana Akufo-Addo
  • Nana Akufo-Addo ya dira fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja, a yau Talata, 22 ga watan Fabrairu
  • Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasar ya kammala ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin takwaransa na kasar Ghana, Nana Akufo-Addo a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Buhari ya tarbi shugaban na kasar Ghana ne jim kadan bayan gama ganawarsa da gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu.

Babban bako a villa: Buhari ya karbi bakuncin takwaransa na kasar Ghana
Shugaban kasa Buhari ya karbi bakuncin takwaransa na kasar Ghana Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Labarin ganawar shugabannin na kasashen Afrika biyu na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara a kafofin sadarwa ta zamani, Buhari Sallau ya fitar a shafinsa na Twitter.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gwamnonin APC sun amince da sabuwar ranar zaben shugabannin jam'iyya

Sai dai babu wani cikakken bayani game da abun da shugabannin za su tattauna a kai a daidai lokacin kawo wannan bayanin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari sallau ya rubuta a shafin nasa:

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Ghana mai girma Nana Akufo-Addo a fadar gwamnati a ranar 22 ga watan Fabrairu.”

Gwamnonin APC sun shiga ganawar gaggawa da Shugaba Buhari

A gefe guda, mun kawo a baya cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar gaggawa da gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a dakin taron fadar Shugaban kasa Aso Villa, Abuja.

Wadanda ke hallare a ganawar sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, da wasu gwamnoni 18, rahoton DailyTrust.

Daga cikin gwamnonin akwai na Yobe, Kano, Kogi, Ekiti, Nasarawa, Kwara, Ebonyi, Jigawa, Lagos, Imo, Ogun, Borno, Niger, Gombe, Osun, Kebbi, Plateau, da kuma mataimakin gwamnan Anambra.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dawo gida daga Brussels, Belgika

Ana zaman ne bisa dage taron gangamin jam'iyyar da Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, yayi wanda ya bar baya da kura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel