Bai hallata mace 'yar sanda ta dau juna biyu ba muddin ba tada aure, Kotu ta yanke

Bai hallata mace 'yar sanda ta dau juna biyu ba muddin ba tada aure, Kotu ta yanke

  • Kotu ta yanke hukunci kan lamarin haramtawa mata yan sanda daukan juna biyu kafin suyi aure
  • Kwanakin baya hukumar ta sallami wata jami'ar yan sanda a Ekiti don ta dau juna biyu kuma ba tada aure
  • Kungiyar lauyoyi, yan fafutuka da sauransu sun lashi takobin kwato mata hakkinta

Babban kotun tarayya dake Abuja ta yi watsi da karar da kungiyar lauyoyin Najeriya NBA ta shigar don cire wasu dokokin hukumar yan sanda da suka haramtawa mace mara aure daukar ciki.

NBA ta shigar da karan ne bisa hujjar cewa doka ta 127 na hukumar yan sanda ta sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya kuma zalunci ne ga mata yan sanda.

Dokar tace: "mace yar sanda mara aure, wacce ta dau ciki, za'a koreta daga hukumar kuma ba za'a sake daukarta ba sai IG ya bada umurni."

Kara karanta wannan

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

NBA ta shigar da kara ne bisa 'yar sanda, Omoloja Olajide, da aka kora daga hukumar ranar 26 ga Junairu, 2021, a jihar Ekiti.

Mata Yan Sanda
Bai hallata mace 'yar sanda ta dau juna biyu ba muddin ba tada aure, Kotu ta yanke
Asali: Facebook

Martani kan karar, Antoni Janar na kasa, ya bukaci kotu tayi watsi da karar.

Antoni Janar yace abinda ya kamata kungiyar NBA tayi shine ta tafi wajen majalisar dokokin tarayya don a canza dokar.

Alkali Inyang Ekwo, a ranar Litinin ya yanke hukuncin watsi da karar, rahoton TheCable.

A cewarsa, karar ba tada wani amfani saboda mata yan sandan sun san da dokar kafin su shiga hukumar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel