Kwankwaso, tsaffin gwamnoni, yan siyasa sun kaddamar da sabuwar kungiyar siyasa TNM

Kwankwaso, tsaffin gwamnoni, yan siyasa sun kaddamar da sabuwar kungiyar siyasa TNM

  • Tsohon gwamnoni, ministoci, Sanatoci sun yi bara'a daga APC da PDP sun kafa sabuwar tafiyar siyasa TBN
  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce har zuwa yanzu shi cikakken ‘dan jam’iyyar adawa ya PDP
  • Wannan taro ya gudana a babban dakin taron International Conference Center ICC dake Abuja

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tare da wasu jiga-jigan siyasa a Najeriya sun kaddamar sabuwar kungiyar siyasa mai suna The National Movement TNM.

A yanzu dai, kungiyar rashin kawo sauyi Najeriya ne amma ana hasashen za ta iya rikidewa ta koma jam'iyyar siyasa.

Wadanda ke halarce a taron sun hada Alhaji Tanko Yakasai, tsohon Gwamnan Kogi Capt Idris, da Injiniya Buba Galadima.Sauran sun Air Vice Marshall Ifeanaju; Solomon Edoda; Nweze Onu; Falasade Aliyu; Rufai Alkali; Suleiman Hunkuyi; Sanata Grace Bent; Umale Shittu; Ibrahim Ringim; Ali Gwaska; Paul Okala; Rufai Hanga; Idris Wada; Abdulrahman Abubakar, dss.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, tsohon ministan Buhari: Jerin yan siyasar da suka kafa sabuwar kungiyar siyasa

Kwankwaso a jawabin da yayi ya ce wasu ƴan Najeriya da suka damu da abin da ke faruwa a Najeriya suka haɗa kai dan kafa kungiyar don ceto ƙasar daga halin da take ciki.

Kwankwaso
Kwankwaso, tsaffin gwamnoni, yan siyasa sun kaddamar da sabuwar kungiyar siyasa TNM Hoto: BBC
Asali: UGC

Har yanzu ina PDP

Sanata Rabiu Kwankwaso a wata hira da ya yi da BBC Hausa, ya tabbatar da cewa bai sauya-sheka daga jam’iyya PDP kamar yadda wasu mutane ke tunani ba.

Kwankwaso ya ce The National Movement kungiya ce ba jam’iyyar siyasa ba, wanda suka kafa domin ganin an fitar da Najeriya daga halin da take ciki a yanzu.

Yace ba jam’iyya ba ce, kungiya ce da suka yi ta domin tafiyar da jama’a a kan layin shugabanni na kwarai.

Shekara guda kenan mu na tattaunawa da mutanen da muke ganin ya dace mu tattauna da su, cewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel