An tsare ni ba bisa ka’ida ba: Abba Kyari ya nemi diyyar N500m a hannun NDLEA

An tsare ni ba bisa ka’ida ba: Abba Kyari ya nemi diyyar N500m a hannun NDLEA

  • Tsohon shugaban rundunar leken asiri ta IRT, Abba Kyari na neman hukumar NDLEA ta biya shi diyyar naira miliyan 500
  • Kyari ya bukaci hakan ne kan zargin cewa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyin ta kasa ta kama shi da kuma tsare shi ba bisa ka'ida ba
  • Ya kuma bukaci kotu ta umurci NDLEA da ta bashi hakuri ta hanyar rubutu a jaridun kasar biyu

DCP Abba Kyari ya nemi hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta biya shi diyyar naira miliyan 500 kan zargin kama shi da tsare shi ba bisa ka’ida ba.

Kyari, a cikin karar da ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22, ya kuma nemi kotu ta umurci NDLEA da ta bashi hakuri ta hanyar rubutu a jaridun kasar guda biyu, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan ƙodarta ta yi ɓatan dabo daga zuwa Saudiyya, za a biya ta N31.8M diyya

An tsare ni ba bisa ka’ida ba: Abba Kyari ya nemi diyyar N500m a hannun NDLEA
An tsare ni ba bisa ka’ida ba: Abba Kyari ya nemi diyyar N500m a hannun NDLEA Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cikin karar da ya shigar ta hannun lauyar sa, C. O. Ikenna, Kyari ya kuma nemi umarnin:

"Hana wanda ake kara (NDLEA), jami’anta, jami’an tsaro, ‘yan sanda ko duk wanda ke wakiltar su daga ci gaba da cin zarafi, tsarewa, tsoratarwa, da kama mai kara ba bisa ka'ida ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Hukuncin kotu da ke umurtan wanda ake kara da ya biya diyyar N500,000,000.00 (naira miliyan dari biyar) ga wanda ke kara, kan tauye hakkin wanda ke kara wanda yake a sashi na 35 da 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya (kamar yadda aka gyara)."

Ya kuma bukaci a ayyana kama shi da ci gaba da tsare shi da NDLEA ke yi ba tare da kai shi gaban kotu ba tun daga ranar 12 ga watan Fabrairu har zuwa yanzu a matsayin wanda baya bisa ka’ida da kuma tauye masa yancinsa, The Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sharri aka min, ina da ciwon sukari da hawan jini: Abba Kyari ya kai karar gwamnati kotu

Ya ce sashe na 35(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da kuma sashe na 6 na dokar kare hakkin dan Adam da jama’a ta Afirka ta tabbatar da yancinsa da kuma damarsa ta yin walwala.

Sharri aka min, ina da ciwon sukari da hawan jini: Abba Kyari ya kai karar gwamnati kotu

A gefe guda, mun ji cewa DCP, Abba Kyari, wanda a halin yanzu yake hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, bisa zarginsa da hannu a safarar miyagun kwayoyi, a ranar Litinin, ya maka gwamnatin tarayya a kotu, Vanguard ta ruwaito.

Kyari, a cikin karar da ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22, yana rokon kotu da ta tilasta wa hukumar NDLEA ta bayar da belinsa bisa dalilan rashin lafiya, har zuwa lokacin da za a saurari kararsa tare da yanke hukuncin neman tabbatar laifinsa.

Kara karanta wannan

Ana ta bincike: Hukumar 'yan sanda ta dakatar da 2 daga cikin abokan harkallar Abba Kyari

A cikin karar da ya shigar ta hannun lauyar sa, Mrs PO Ikenna, tsohon shugaban rundunar leken asiri ta IRT, ya shaida wa kotun cewa ana tsare da shi ne “saboda zargin karya da aka kakaba masa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel