Zaben 2023: Tunda Musulmi ya dana, ya kamata a ba Kirista ma ya dana, inji CAN

Zaben 2023: Tunda Musulmi ya dana, ya kamata a ba Kirista ma ya dana, inji CAN

  • Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta tsaya tsayin daka kan kiran da ta yi na neman a samar da shugaban kasar Kirista a zaben 2023 mai zuwa
  • Rabaran Samson Ayokunle, Shugaban CAN ya gargadi jam’iyyun siyasa da su guji fitar da tikitin takarar shugaban kasa na Kirista da Kirista ko Musulmi da Musulmi
  • Ayokunle ya yi kira da a mara wa shugabannin siyasa na Kirista baya a dukkan shiyyoyin siyasar kasar nan don tabbatar da manufarsu

Jos, jihar Filato - Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta sha alwashin hada kan dukkan Kiristocin kasar nan domin samar da wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari.

Jaridar New Telegraph ta ruwaito cewa shugaban CAN, Rabaran Dr. Samson Ayokunle wanda ya bayyana hakan ya ce duk wani tikitin da zai dauki Musulmi da Musulmi ko Kirista da Kirista ba za ta amince da shi ba.

Kara karanta wannan

Kun mayar da lakcarori bayi: ASUU ta caccaki gwamnatin Buhari kan batun albashi

Kungiyar Kiristoci ta tubure, ta ce dole a samar da kirista ya gaji Buhari
Zaben 2023: Tunda Musulmi ya dana, ya kamata a ba Kirista ma ya dana, inji CAN | Hoto: thenigerianvoice.com
Asali: UGC

Rabaran Ayokunle ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Fabrairu, yayin wata tattaunawa da aka yi da shi bayan wa’azinsa a majami'ar COCIN da ke Rahwol Kanang a Jos ta Jihar Filato.

Ya nemi hadin kan shugabannin siyasa na Kirista a shiyyoyin siyasa guda shida don tabbatar da wannan manufa ta CAN.

A cewarsa, Kiristoci na da yawan al’umma da za su iya zarce yawan kuri’un da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a zaben 2019.

Ya bayyana Kiristoci da Musulmi a matsayin jiga-jigan da ke kan ganawa a harkokin tafiyar da Najeriya domin babu wani addini da zai iya barin daya a fannin siyasa ya yi nasara shi kadai.

Shafin yada na LindaIkeji ta tattaro shi yana cewa:

"Ina son duka Kirista da Musulmi su fahimci juna su tsayar da wanda zai ci gaba da rike mu tare da kasa baki daya."

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Saraki ya cancanci darewa kujerar Buhari, in ji kungiyar matasa

Ya jaddada cewa hadin kan Kiristoci a Najeriya shi ne alherinsu, raba kansu kuma shi ne faduwarsu, ya kara da cewa ya kamata su hada kai domin kawo shugaba Kirista.

2023: Na shirya kazamin artabu da kowa, babu abinda zai razana ni, Tinubu

A wani labarin, dan takarar shugabancin kasa karkashin All Progressives Congress, APC, Bola Tinubu, a ranar Lahadi ya sha alwashin cewa babu wata razanarwa ko barazana da za ta dakile masa burin zama shugaban kasa.

Ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi da kuma zababben Olubadan, Oba Lekan Balogun.

A watan Janairu Tinubu ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bayyana shirinsa na fitowa takara a zaben 2023, Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel