Sojojin Najeriya sun kashe Buba Danfulani da kwamandojin ISWAP 4 a Sambisa

Sojojin Najeriya sun kashe Buba Danfulani da kwamandojin ISWAP 4 a Sambisa

  • Sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a sansanonin yan ta'adda a yankunan Tumbuns da Sambisa a arewa maso gabas
  • Harin ya kai ga halaka Amir Buba Danfulani da wasu manyan kwamandojojin ISWAP hudu
  • Sai dai zuwa yanzu babu wata sanarwa daga rundunar sojin Najeriya da ke tabbatar da al’amarin

Ruwan bama-bamai da jirgin yakin sojin Najeriya ta yi ya halaka Amir Buba Danfulani da wasu tsagerun kwamandojin ISWAP hudu a yankunan Tumbuns da Sambisa a arewa maso gabas.

PRNigeria ta tattaro cewa Amir Buba Danfulani ya kasance babban kwamandan ISWAP wanda ke aikin koyawa Fulani da makiyaya shiga kungiyar ta’addanci. Ya kuma jagoranci ayyukan ‘yan ta’adda kama daga diban ‘yan leken asiri da kuma masu karbar haraji.

Rundunar sojojin Najeriya karkashin Operation HADIN KAI ce ta aiwatar da hare-haren a wurare daban-daban a cikin makon.

Kara karanta wannan

Jirgin yaki ya ragargaji 'yan ISWAP a Marte, sojoji da dama sun jikkata a Abadam

Sojojin Najeriya sun kashe Buba Danfulani da kwamandojin ISWAP 4 a Sambisa
Sojojin Najeriya sun kashe Buba Danfulani da kwamandojin ISWAP 4 a Sambisa Hoto: PRNigeria
Asali: UGC

Wata majiyar sirri ta bayyana cewa, an girke jiragen Super Tucano, jirage masu saukar ungulu da sauran jiragen yaki a hare-haren na tsawon mako guda da aka gudanar a wurare daban-daban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce kafin aiwatar da harin na musamman, binciken sirri ya gano sansanonin yan ta’adda a Tumbun Kaiyowa da Tumbun Allura wanda ke cike da ayyukan ISWAP da Boko Haram.

Ta kuma ce yan ta’adda na kuma amfani da sansanonin wajen harba makamai masu linzami a wuraren sojojin Najeriya da ke Mallam Fatori.

Don haka sai rundunar Operation Hadin Kai ta tura jiragen yaki wanda ya yi raga-raga da yan ta’addan domin hana su ci gaba da kaiwa sojoji hare-hare.

Majiyar ta kara da cewa:

“Jiragen yakin sun saki bama-bamai da dama a Tumbun Kaiyowa da ruwan rokoki a Tumbun Allura. Jirage masu saukar ungulu suka kuma shafe yan ta’addan da suka tsere.

Kara karanta wannan

Ana ta bincike: Hukumar 'yan sanda ta dakatar da 2 daga cikin abokan harkallar Abba Kyari

“Hakazalika an aiwatar da harin a Parisu da Njimia kewayen jejin Sambisa, inda jiragen yaki uku mabanbanta suka yi barin wuta kan yan ta’addan."

PRNigeria ta tattaro daga majiyoyi cewa shugabannin yan ta’adda biyar aka kashe a harin. Sun hada da Musa Amir Jaish, Mahd Maluma, Abu-Ubaida, Abu-Hamza da kuma Abu-Nura umarun Leni.

Sai dai babu wata sanarwa kawo yanzu daga rundunar sojin Najeriya da ke tabbatar da al’amarin.

Harin jirgin yakin Najeriya ya kashe yara bakwai a Jamhuriyar Nijar

A gefe guda, mun ji cewa wani hari ta sama da rundunar sojin Najeriya ta kai kan yan bindiga ya kashe kananan yara bakwai sannan ya jikkata wasu biyar bisa kuskure a kasar Nijar.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wani gwamnan kasar ne ya sanar da kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP hakan a ranar Lahadi, 20 ga watan Fabrairu.

A cewar gwamnan, iyayen yaran na halartan wani taro ne sannan yaran kuma suna cikin wasa lokacin da harin ya riske su, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Kusoshin Gwamnati za su amsa tambayoyi a Majalisa kan zargin cuwa-cuwar albashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel