Jirgin yaki ya ragargaji 'yan ISWAP a Marte, sojoji da dama sun jikkata a Abadam

Jirgin yaki ya ragargaji 'yan ISWAP a Marte, sojoji da dama sun jikkata a Abadam

  • Harin bama-bamai da sojojin Najeriya suka kai ta sama ya hallaka mayakan ISWAP 34 a garin Marte na jihar Borno
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji tara suka samu munanan raunuka sakamakon karo da suka yi da wasu nakiyoyi da 'yan ta'adda su ka binne a garin Malam Fatori
  • Sojojin na shirin kai hari ne kan wasu mayakan ISWAP da ke taruwa a Tumbun Dan Katsina

Borno - Hare-haren bama-bamai ta sama da rundunar sojojin sama suka kai ya kashe yan ta’adda 34 a garin Marte da ke jihar Borno, PRNigeria ta rahoto.

Hakan na zuwa ne adaidai lokacin da sojojin kasa su tara suka jikkata a lokacin da ayarin motocinsu ya taka wani dam da yan ta’addan suka binne a karkashin kasa a Malam Fatori a karamar hukumar Abadam da ke jihar.

Kara karanta wannan

Ana ta bincike: Hukumar 'yan sanda ta dakatar da 2 daga cikin abokan harkallar Abba Kyari

Jirgin yaki ya ragargaji 'yan ISWAP a Marte, sojoji da dama sun jikkata a Abadam
Jirgin yaki ya ragargaji 'yan ISWAP a Marte, sojoji da dama sun jikkata a Abadam Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: UGC

An tattaro cewa dakarun na kokarin kai hari kan mayakan ISWAP da ke Tumbun Dan Katsina lokacin da lamarin ya afku.

A halin da ake ciki, an tattaro cewa dakarun NAF tare da hadin gwiwar jami’an hadin gwiwa na MNJTF, a ranar Laraba, sun aiwatar da wasu hare-hare ta sama a sansanonin mayakan ISWAP a Sabon Tumbu da ke karamar hukumar Marte.

Wata majiya ta tsaro ta ce harin da sojojin suka kai ya biyo bayan wani bayanai da suka samu cewa an gano mayakan ISWAP kimanin su 100 cikin jirgin ruwa a Sabon Tumbu.

Majiyar ta tabbatar da cewar jirgin yakin Super Tucano da aka tura aikin, ya ragargaji mabuyar yan ta’addan inda ya kashe da yawa daga cikinsu, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An sake yi wa matafiya 'yan Kano da Nassarawa kisar gilla a hanyar Jos

Ya kara da cewa ci gaba da kai hare-hare ta sama ya yi tasiri kan yan ta’addan, tare da dakile shirinsu na kai wasu manyan hare-hare a kan sansanonin sojoji a kewayen Malam Fatori, Damasak, Gubio da Kauwa.

Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe 'yan ISWAP da B/H 120, sun kamo 50, sun kwato makamai

A gefe guda, dakarun rundunar sojojin Najeriya karkashin atisayen Operation HADIN KAI sun kashe mayaka 120 a cikin yan makonnin da suka gabata.

Daraktan yada labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 10 ga watan Fabrairu, a taron manema labarai wanda wakilin Legit.ng ya halarta a Abuja.

Ya ce dakarun sun kuma kama yan ta’adda 50, sannan suka kwato motocin harbi guda 5, makamai iri-iri guda 50 da kuma alburasai daban-daban guda 200 daga yan ta’addan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel