'Yan bangan siyasan Matawalle sun kai mana farmaki a kotu, Hadimin Marafa

'Yan bangan siyasan Matawalle sun kai mana farmaki a kotu, Hadimin Marafa

  • Sakataren yada labarai na Sanata Marafa, Bello Bakyasuwa, ya koka kan farmakin da 'yan bangan siyasan Gwamna Matawalle suka kai masa
  • Ya yi kira ga jami'an tsaron da ke jihar da su yi aikinsu ta hanyar tsamo wadanda suka kai masa farmaki ko kuma su faara baiwa kansu kariya
  • A cewar Bakyasuwa, miyagun 'yan bangana siyasan suuna farautar rayukansu babu kakkautawa tare da lauyansu

Zamfara - Sakataran yada labaran sanata Kabiru Garba Marafa na tsagin jam'iyyar APC a Zamfara, Bello Bakyasuwa, ya yi kira ga jami'an tsaro da su tsare musu rayukan su daga hare-haren da 'yan bangan siyasan Gwamna Bello Matawalle ke kai musu ba kakkautawa.

Bakyasuwa, wanda ya zanta da manema labarai bayan zaman da aka yi a babban kotun Gusau dake jihar Zamfara, ya koka game da yadda 'yan bangan siyasan Matawalle ke kai wa lauyan su da shi kanshi farmaki a cikin harabar kotun.

Kara karanta wannan

Ku mika wuya tun kafin mu iso maɓoyarku, Sabon Kwamishina ya aike da sako ga yan bindiga

'Yan bangan siyasan Matawalle sun kai mana farmaki a kotu, Hadimin Marafa
'Yan bangan siyasan Matawalle sun kai mana farmaki a kotu, Hadimin Marafa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Inda yake bayyana cewa, ba wanda aka kama, ya yi kira ga jami'an tsaro da su tsaya bakin aikin su.

Kamar yadda rahoton Punch ya bayyana, ya ce daga yanzu, tsagin Kabiru Marafa za su kare kawunan su, idan jami'an tsaron basu kawo musu dauki ba.

"Zan so in yi kira ga jami'an tsaron Najeriya cewa daga yanzu, idan aka kara kai mana hari irin wannan ko aka yi kokarin kai mana, ba mu da wani zabi idan ba mu kare kawunan mu ba idan har hukumomi ba za su iya kare mu ba.
"Haka zalika, muna bukatar 'yan sanda su gaggauta zakulo wadanda ke da alhakin wannan harin, saboda mun yi imani da cewa sun san su," Bakyasuwa ya kara.

Yayin martani ga ikirarin Bakyasuwa, sakataran watsa labarai APC na jihar, Yusuf Idris, ya ce labarin kanzon kurege ne, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kisan Hausawa dillalan shanu a Kudu: Kungiyoyin Arewa sun fusata, sun tura gargadi ga gwamnatin Abia

Idris ya ce, da mamaki a ce mutum kamar Bakyasuwa ya iya zabga karairayi, inda ya tabbatar da cewa ya halarci kotun, kuma ya zauna wuri daya da Bakyasuwa, amma babu wanda ya kaimasa hari.

Zamfara APC: Rikici ya dauka sabon salo, ana amfani da 'yan daba wurin kai farmaki

A wani labari na daban, rikicin cikin gida na cigaba da rincabewa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta jihar Zamfara inda sabon salo ya kunno kai a cikin tsagi daban-daban na jam'iyyar ta yadda ake daukar nauyin kai farmaki da 'yan daba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, tsagin tsohon gwamna Abdulaziz Yari ya nuna firgici da tashin hankali a jihar inda suke zargin za a mayar da jam'iyyar filin daga inda 'yan daba ke baje-kolin su.

Shugaban tsagin, Lawal M. Liman, wanda ya yi wannan hasashen, ya bayyana cewa, farmakin kwanan nan da aka kai wa shugaban fannin yada labarai na kafafen sada zumuntan Sanata Kabiru Gwarba Marafa na jam'iyyar, Malam Shamsu Shehu datsakar rana ya zama abun tashin hankali ga duk mai san zaman lafiya da kiyaye doka a jihar.

Kara karanta wannan

Yadda IGP da Marwa suka gana, suka shirya yadda za a damke Abba Kyari da mukarrabansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel