Karar kwana: Mutane 17 sun kone kurmus yayin da tankar mai ta kama da wuta

Karar kwana: Mutane 17 sun kone kurmus yayin da tankar mai ta kama da wuta

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, wata tankar mai ta yi hadari, inda mutane har 17 suka rasa rayukansu
  • Hukumar kula da haddura ta jihar Ogun ta bayyana cewa, ba a iya gane fuskokin wadanda suka mutu ba
  • Ya zuwa yanzu, hukumar ta ce tana ci gaba da bincike don tantance wadanda suka rasa rayukansu

Jihar Ogun - Jaridar Punch ta ruwaito cewa, akalla mutane 17 ne suka kone kurmus a yau Juma’a, yayin da wata tankar mai ta kama wuta a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a jihar Ogun.

Hukumar kiyaye hadurra ta FRSC ta tabbatar da cewa hatsarin ya afku ne da misalin karfe 5 na safiyar ranar Juma’a kafin isa gadar Isara.

An yi hadari a jihar Ogun
Innalillahi: Mutane 17 sun kone kurmus yayin da tankar mai ta kama da wuta | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Mai magana da yawun FRSC a Ogun, Florence Okpe, ta bayyana cewa 14 daga cikin gawarwakin sun kone ba ta yadda ba za a iya gane su ba, inda ta kara da cewa jami’an FRSC sun iya gane namiji daya, mace daya da kuma wata yarinya.

Kara karanta wannan

Kamar a jahiliyya: Uba ya kashe 'ya'yansa tagwaye, za a rataye shi har sai ya mutu

Ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ba a tabbatar da adadin mutanen da lamarin ya shafa ba, amma an gano gawarwaki 17 (da suka mutu).
“An gano namiji daya, mace daya, da kuma yarinya mace daya, yayin da akwai wasu da suka kone ba a iya gane su ba.”

Da yake bayyana abin da ya haddasa faruwar lamarin, Okpe ya ce tankar ta yi karo ne da wata motar bas Mazda mai lamba ZT728 KLD.

Ta ce:

“Abubuwan da ake zargin sun haddasa hatsarin sun hada da keta dokar hanya da kuma tukin ganganci, wanda ya haifar da karo da tashin wuta.

A halin da ake ciki, Kwamandan Hukumar FRSC na Jihar Ogun, Ahmed Umar, ya bayyana hadarin a matsayin abin da za a iya kauce masa, inda ya bukaci a ke taka-tsantsan da bin ka’idojin tuki.

Kara karanta wannan

Harkallar kwaya: Abba Kyari ya yi fallasa, NDLEA ta je kotu neman ci gaba da tsare shi

Umar ya jajanta wa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, inda ya umurce su da su tuntubi ofishin FRSC da ke Ogere domin karin bayani game da hadarin, kamar yadda Independent ta tattaro.

Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

A wani labarin, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wani yaro mai suna Sulaiman Usaini dan shekara daya da mahaifiyarsa mai suna Zainab Yusha’u mai shekaru 25 a hanyar Gwarzo da ke Gidan Kaji a jihar Kano.

Alhaji Saminu Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na hukumar ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kano, Daily Trust ta ruwaito.

Abdullahi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar Asabar 8 ga watan Janairun 2022.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel